Kansilolin jam’iyyar APC a ƙarƙashin ƙungiyarsu ta NPCF su amince da naɗin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.
Kansilolin bisa jagorancin Hon Muslihu Yusuf Ali, sun bayyana haka ne cikin sanarwar manema labarai da suka fitar mai ɗauke da sa hannnun Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Hon Abayomi A. Kazeem a ranar Asabar.
Kansilolin sun ce bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar ya yi daidai kasancewarsa gogaggen ɗan siyasa, ƙwararre wanda ya samar da ɗimbin ci gaba a Jihar Kano a zamanin gwamnatinsa.

Ƙungiyar kansilolin ta nuna godiyarta ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da zaɓa wa jam’iyyarsu ta APC mutumin ƙwarai a matsayin jagora.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp