Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, N’Golo Kante ya sayi kungiyar kwallon kafa ta Royal Edcelsior Birton da ke mataki na uku a gasar kwallon kafar kasar Belgium.
Dan kwallon na Faransa mai shekaru 32, zai maye gurbin Flabio Becca a matsayin shugaban kungiyar daga ranar 1 ga watan Yuli kuma shi ne zai ci gaba da kula da lamuran kungiyar.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Yi Wa Jama’a Kutse A Asusun Banki
- Daliban Najeriya 65 Sun Samu Gagarumar Tarba Bayan Kammala Shirin Tallafin Karatu A Sin
Kante ya bar Chelsea inda ya kulla yarjejeniya da kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya bayan ya sha fama da ciwo a Chelsea wanda hakan ya sa bai samu damar buga wasanni ba a kakar da ta gabata.
Shugaban kungiyar na yanzu “Flabio ya ce yana cikin matukar jin dadin da zai mika ragamar kungiyar ga N’Golo Kante kuma yana ganin Kante zai ci gaba da jagorantar kungiyar yadda ya kamata.
Kungiyar na kokarin komawa matakin farko a gasar kwallon Belgium wanda hakan ya sa ake ganin kungiyar take bukatar mamallakin da za dora kungiyar akan layi mai dorewa.
Kante ya soma buga wasa ne a karamar kungiyar Boulogne a Faransa kafin ya koma Caen a shekara ta 2013 daga baya ya koma kungiyar Leicester City inda ya taimaka wa kungiyar lashe gasar Premier a 2016 kafin ya koma Chelsea inda ya lashe gasar zakarun Turai da kuma na Premier da kofin FA.