Jagoran tsagerun Igbo masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, ya yi tir da hare-haren da wasu ke kai wa yankin kudu maso gabas a ‘yan kwanakan nan.
Kanu, ya sanar da hakan ne ta hanyar lauyansa na musamman Aloy Ejimakor a lokacin da Ejimakor ya jagoranci wasu ‘ya’yan tawagar lauyoyin da ke tsayawa Kanu, inda suka yi ganawar da suka saba yi da shi a ofishin jami’an tsaro na cikin gida DSS, inda ake tsare da shi.
Jagoran ya kuma jajanta wa wadanda hare-haren suka rutsa da su.
Ejimakor ya sanar da sakon na Kanu ne a shafinsa na sada zumunta na twitter, inda ya ce, Kanu ya nuna takaicinsa akan hare-haren, ciki har da harin da aka kai a mahaifarsa ta haihuwa.
A ‘yan kwanukan nan dai, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka kai hare-hare akan al’umma, kasuwanni da kuma gine-ginen gwamnati da ke yankin kudu maso gabashin kasar nan, inda ko a kwanakin baya, ‘yan bindigar sun kai wasu hare-haren akan ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC da ke yankin.