Damisar takarda tana da ban tsoro, amma ba ta da karfi.
A wajen taron ministocin harkokin waje na kasashen BRICS da kasashe abokanta, da ya kammala jiya Talata, a kasar Brazil, mahalarta taron sun gabatar da wata sanarwa, inda suka nuna damuwa kan wasu matakan kashin kai da suka saba wa ka’idojin kungiyar ciniki ta duniya WTO, wato matakan karbar karin harajin fito, da ta da yakin ciniki, da kasar Amurka ta aiwatar.
- Xi Jinping Ya Karfafawa Matasa Gwiwar Daukar Nauyin Daukaka Zamanantar Da Kasar Sin
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
Da yake jawabi, ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana matsayar Sin dangane da batun. Ya ce, “Amurka ta dora moriyarta sama da moriyar bai daya ta kasashen duniya.” “Amurka ta dade tana ci riba mai tsoka daga cinikin da ta yi da sauran kasashe, amma yanzu ta yi amfani da harajin fito a matsayin makami, wajen tilastawa sauran kasashe biyanta kudi. Idan an yi hakuri da matakin, to, Amurkar za ta kara cin zarafin sauran kasashe.” To, wannan maganar da Wang Yi ya fada ya nuna dalilin kasar Sin na daukar kwararran matakan ramuwar gayya bisa matakin Amurka na karbar karin harajin fito.
Kasar Sin ba za ta mika wuya ba, saboda tana tsayawa kan adalci. Sinawa su kan ce, “Wanda ke tare da adalci ba zai rasa abokan da za su taimaka masa ba.” To, yadda mambobin BRICS, da kasashe abokan BRICS, suka dauki ra’ayi daya a wannan karo, ya shaida gaskiyar maganar. Ban da haka, a gefen taron na wannan karo, minista Wang Yi na Sin ya gana da Yusuf Tuggar, ministan wajen kasar Najeriya. Kuma a madadin gwamnatin kasar Najeriya, mista Tuggar ya yabi kasar Sin bisa yadda ta dauki nauyin kare tsarin duniya na kasancewar mabambantan bangarori, da kiyaye moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa.
To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar Amurka suna samun goyon baya tsakanin al’ummun kasashe daban daban, inda a dimbin kasashe masu tasowa da suka hada da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Ghana, da Afirka ta Kudu, da Turkiya, matakan kasar Sin suka samu goyon baya daga mutane fiye da kaso 70% da aka gudanar da bincike kansu. Kana a kasashen yamma da suka hada da Faransa, da Jamus, da Canada, da Birtaniya, da dai sauransu, jimillar ta kai tsakanin kaso 65.5% zuwa 70.5%.
Sai dai kasar Sin ba ta son yakin ciniki, ko da yake tana wakiltar ra’ayi mai adalci na akasarin kasashe. Kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, “Babu mai samun nasara a yakin harajin fito, da na ciniki.” Amma, bisa la’akari da cewa kasar Amurka ce ta ta da yakin ciniki, to, kasar Sin ba za ta taba mika wuyarta ba, kuma ba za ta yi hakuri da matakin cin zarafi ba. Sin ta nanata cewa, idan kasar Amurka na son daidaita al’amarin ta hanyar tattaunawa, to, ya kamata ta “daina barazana da matsin lamba, ta yi tattaunawa bisa tushen daidaito, da mutunta juna, da amfanawa juna.”
Hakika, ban da wadannan abubuwan da aka ambata, don kaddamar da tattaunawa, ana bukatar sanin ya kamata, wanda kasar Amurka ta rasa. Misali, yadda kasar Amurka ta janye jikinta daga dimbin kungiyoyin kasa da kasa, da yarjeniyoyin duniya, da daina samar da tallafi ga sauran kasashe, sun nuna yunkurinta na kaucewa daukar nauyi sakamakon raguwar karfinta a fannin tattalin arziki. Sai dai wannan yanayi mai kunci bai hana ta ci gaba da neman ba da umarni ga sauran kasashe, da cin zarafinsu ba. Ban da haka, mu kan ga yadda shugabannin kasar Amurka suke ba da umarni da gyara shi cikin sauri, da yin karairayi yadda suka ga dama, da wulakanta takwarorinsu na sauran kasashe, da kasa kare bayanan sirrin da suka shafi yaki, wadanda suka nuna gazawarsu wajen aiki. Ma iya cewa, yanzu haka, kasar Amurka tamkar damisar takarda ce, mai ban tsoro amma maras karfi.
Za mu jira lokacin da za a iya komawa teburin shawarwari don tattauna batun kawo karshen yakin ciniki, inda za a jira har zuwa lokacin da kasar Amurka za ta gamu da dimbin matsaloli, ta yadda za ta yi watsi da matakan zalunci, da sake samun sanin ya kamata. Amma yanzu muna iya tabbatar da matakin da ya kamata kasashe masu tasowa su dauka, wato karfafa hadin kansu, maimakon mika wuya ga kasar Amurka, wadda ta kasance tamkar wata “damisar takarda”, da ke neman cin zarafin sauran kasashe, da ta da rikici a duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp