Aure amana ce, kuma mace ita ce ginshikin gidan aure. Duk abin da ta aikata na iya zama alkhairi ko sharri ga kanta. Sau da yawa, mata suna yin wasu kananan kusakurai da ba su ga muhimmancin su ba, amma daga baya sai su gane cewa sun rasa abu mafi daraja, son mijinsu da girmamawarsa.
Akwai lokutan da mace kan yi abin da take so ba tare da ta kula da tasirinsa ba, daga baya sai ta yi kuka da nadama. Ki tsaya ki karanta wannan sosai, domin kada ki shiga cikin wannan jerin mata da suke rayuwa cikin nadama, ba da dadi ba, da ciwon zuciya.
1. Rashin Girmama Mijinki
Matar da ta daina ganin girman mijinta ta riga ta fara ruguza aurenta, da zarar kin yi masa maganganu na cin mutunci, kin yi kamar kin tozarta kanki da kanki ne, saboda girman mace a cikin aurenta yana da alaka da girman mijinta.
2. Rashin adalci tsakanin mijinki da danginsa
Ki sani, mijinki zai iya jure miki a kuskuren da kike masa kai tsaye, amma zai dade yana daukar zafin abin da kika aikata wa iyayensa, ‘yan uwansa ko danginsa, wannan babban kuskure ne da mata da dama suke yi su kuma yi nadama daga baya.
3. Rashin Tausayi da Kulawa
Ki sani, koda kuwa mijinki yana da kudi, yana bukatar jin tausayi daga gare ki. Idan ya dawo gida a gajiye, kuma ba kya nuna damuwarki ko kulawarki, hakan na iya sanyawa ya ji babu darajarsa a idonki. Wannan ma yana daga cikin manyan kurakuran da ake nadama a kai.
4. Yin kishi nai tauri da rashin amana
Kishin mace al’ada ne, amma idan ya wuce kima, yana canza soyayya zuwa guba. Idan baki yarda da mijinki ba, kina tuhumarsa a kan kowanne abu, to ke da kanki za ki gaji, shi ma ya gaji, sai aure ya fara tangal-tangal.
Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa In Allah Ya Kai Mu