Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk wani zargi na cutar murar tsuntsaye (bird flu) ga hukumomin da abin ya shafa.
Wannan ya biyo bayan rahoton wani matashi daga ƙaramar hukumar Gwale wanda ya siyo Agwagwa daga kasuwar Janguza a watan Disamba 2024, wanda daga baya ya lura tsuntsayensa suna fama da wahalar numfashi da kuma mutuwar 35 daga cikin 50 na tsuntsayen shi
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Rikicin Masarautar Kano Ya Sake Daukar Sabon Salo
Bayan gwajin da aka yi a asibitin dabbobi na Gwale, an tabbatar da cutar murar tsuntsaye ce a farkon Janairu 2025. Nan take ma’aikatar aikin gona ta rufe wurin, ta kashe sauran tsuntsayen, tare da tsaftace wuraren kiwo da kasuwanci a kasuwar Janguza. Haka nan, an wayar da kan masu sayar da tsuntsaye game da illar cutar don hana yaduwarta.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya tabbatar wa jama’a cewa ba a kai matsayin ɓarkewar cutar ba. Ya ce ana ɗaukar matakan gaggawa tare da haɗin gwuiwar ma’aikatun aikin gona, muhalli, da albarkatun ruwa don tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma bayyana cewa za a ƙara ƙaimi wajen sa ido a dukkan ƙananan hukumomi domin gano duk wata alama ta cutar.
Kwamishinan ya shawarci masu kiwon tsuntsaye su lura da alamun cutar kamar zazzabi da kumburin idanu a cikin tsuntsayensu. Ya buƙaci su sanar da hukumomi idan sun ga wata matsala domin daukar matakin gaggawa. Haka kuma, ya ce gwamnati za ta ci gaba da sanar da jama’a game da halin da ake ciki tare da daukar matakan
kariya.