Gwamnatin Tarayya na shirin kafa rundunar soji mai karfi a yankin tafkin Chadi, domin inganta samar da abinci a Nijeriya.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ne, ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Talata.
- A Kawo ÆŠauki Don Magance Tsadar KuÉ—in Zuwa Aikin Hajjin Bana
- Kwamandojin Boko Haram 2 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
Shirin na son farfado da aikin noman rani a yankin tafkin Chadi, wanda ke samar wa Nijeriya abinci mai yawan gaske, amma hakan ya durkushe sakamakon ayyukan ta’addancin Boko Haram da ya shafe sama da shekaru 10.
“Yanzu da zaman lafiya ya samu a Jihar Borno akwai bukatar gwamnati ta tabbatar da sake farfado da noman rani a yankin Chadi ta Kudu.
“Na yi magana da shugaban kasa, kuma zai duba yiwuwar kafa rundunar tsaro a yankin tafkin Chadi domin mutane su samu damar zuwa gonakinsu domin yin noma,” in ji Zulum.
Gwamnan ya jaddada aniyar farfado da noman rani a yankin Chadi ta Kudu da ke Arewacin Borno, don magance matsalar karancin abinci da al’ummar kasar nan ke fuskanta.
Zulum ya kuma bayyana cewa ‘yan Nijeriya mazauna kasashen Chadi, Jamhuriyar Nijar, da Kamaru da aka dakatar da dawowa gida sakamakon zabe da damina, za su dawo gida karkashin jagorancin shugaba Tinubu.
Dangane da batun tsaro a makarantu, Zulum ya bayyana cewa, yanzu haka an girke sojoji, Cvilian JTF, mafarauta da kuma ’yan banga a makarantun jihar don bai wa dalibai tsaro.
Gwamnan ya ce a halin da ake ciki gwamnatinsa ta dawo da sama da mutane 100,000 da suka rasa muhallansu zuwa Borno cikin shekaru shida zuwa bakwai da suka wuce, kuma ana sa ran samun karin wasu nan gaba.