Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi kan karancin Naira da makonni biyu.
Kungiyar ta ce hakan zai bayar da damar sanya ido kan matakin da babban bankin Nijeriya (CBN) ke bi a kan yadda ake fitar da kudaden Naira da kuma wadatar da ‘yan Nijeriya.
- Charles Onunaiju: Shawarar Wayewar Kai Ta Duniya Za Ta Haifar Da Alfanu Ga Dan Adam
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 7
Shawarar tsawaita wa’adin ya biyo bayan samun rahotannin da kugniyar kwadago ta samu daga tawagogin sa-ido a fadin Jihohi 36 da daukacin kananan hukumomin da aka tantance babban bankin a kan matakin da ya dace.
A wani taron tattaunawa da aka yi a Abuja ranar Talata bayan kammala taron zartarwa na kasa, shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Kwamared Joseph Ajaero, ya shaida wa manema labarai cewa matsalar kudin na raguwa fiye da baya.
Ya ce, “Bayan kwana daya ko biyu da muka yi muku bayani a nan wakilan CBN sun zo nan. Kuma mun yi ganawa mai amfani da su. Kuma mun ba su shawarwari kan yadda za a magance matsalar, nan da nan suka fara aiki. Kuma abu ya yi kyau.
“Rahotannin da ke fitowa daga duka jihohin tarayya, da kananan hukumomi kan matakin bin bankuna, muna farin cikin sanar da ku cewa eh, akwai suna bin umarnin CBN.
“Bayan taron NEC, mun nuna shakku kan dorewar wannan tsari, kuma ba ma so a sake kiranku bayan kwana biyu, don sanya ido kan wannan doka na tsawon makonni biyu masu zuwa don ganin ko hakan zai dore saboda an tilasta musu fitar da kudi. Bankunan kasuwanci ana sa ran za su dore wajen wadata mutane da kudi,” in ji shi.
A satin da ya wuce ne CBN ya bai wa bankuna umarni yin aiki a karshen mako don wadata mutane da kudi.