Gamayyar Kungiyoyin Sufuri sun yi barazanar yin zanga-zanga a hedikwatar Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), sakamakon karancin man fetur da ake fama da shi.
Sanarwar da suka fitar a ranar Litinin, ta samu sa hannun Jamilu Mai Alheri, Shugaban kungiyar Direbobin Tirela (TADAN), da wasu mutum biyar.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi
- Shugaban Kasar Sin Ya Mika Sakon Jaje Ga Takwarorinsa Na Turkiyya Da Syria Bisa Ibtila’in Girgizar Kasa Da Ya Shafi Sassan Kasashen Biyu
Kungiyoyin sun hadar da Kungiyar Keke Mai Kafa Uku (TOWAN), Kungiyar ‘Yan Kasuwar Nijeriya (NASTAN), ?ungiyar Motocin Kasuwanci ta Nijeriya (COMAN).
Sauran sun hada da Kungiyar Mata ‘Yan Kasuwa ta Nijeriya (MAWAN).
Kungiyoyin dai sun sanya mambobinsu a fadin kasar nan cikin shirin ko ta kwana domin shiga zanga-zangar idan har ba a yi wani abu ba don kawo karshen matsalar karancin mai ba.
Kungiyoyin sun ce za su mamaye manyan gine-ginen NNPCL da ke Abuja har sai an kawo karshen matsalar.
Sun kuma yi barazanar cewa ba za su samar da motocinsu don jigilar kayayyakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) don gudanar da zaben da ke tafe ba.
Kungiyoyin sun koka da cewa karancin man fetur da ake fama da shi ya jefa su cikin wani hali da ba za su iya jurewa ba.
Sanarwar ta ce mambobin sun dogara ne kan samun kudin shiga na yau da kullun daga ayyukansu wanda abin ya shafa.
“Har ila yau, ba za a yi la’akari da cewa ana sayar da man fetur a gidajen da gwamnati ta amince da su a kan Naira 350 zuwa N400 kan kowace lita.
“Wannan ya tilasta wa yawancin mambobinmu daina amfani motocinsu, babura da sauransu,” in ji sanarwar.