Matsalar karancin Mai ko wahalar samunsa na cigaba da zama abun damuwa musamman ga matuka ababen hawa a fadin kasar nan, lamarin da ke kara kuntata wa jama’a hada-hadar rayuwa da zirga-zirga.
Kodayake majalisar wakilai ta tarayya a ranar Talata ya bada wa’adin mako guda tak wa kamfanin Man fetur ta kasa (NNPCL) da ya gaggauta kawo karshen karancin mai da ake fama da shi a kasar nan.
Bugu da kari, baya ma ga matsalar karancin samun man da wahalarsa, al’umma na sayen Man ne kan farashi mabanbanta wanda masu gidajen Man ke tsula farashi fiye da yadda doka ya basu damar sayar da litar Mai ga mabukata.
A umarnin na majalisar ta wakilai, ta kuma bukaci Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa gami da sufurin Man fetur a Nijeriya (NMDPRA) da ta yi aikin hadin guiwa da jami’an tsaron ‘yan sanda da na DSS domin tabbatar da masu sayar da Mai a gidajen mai na sayar da Man bisa farashin da doka ya amince musu.
Matakin kiran na majalisar na zuwa ne bayan wan kudirin da dan majalisa daga jihar Neja Hon Saidu Musa Abdullahi ya gabatar, ya nuna kudirin na da matukar bukatar daukan matakin gaggawa lura da cewa kai tsaye ya shafi al’umma ne.
A cewar Abdullahi watannin da suka gabata al’ummar Nijeriya na fama da matsatsi da kunci gami da wahalar samun mai bisa karancinsa, wanda hakan ya shafi harkokin tattalin arziki kuma ya jefa jama’a cikin garari na wahala.
Ya ce, hukumar kula da Mai fetur ita ke da alhakin sakacin da har ya jawo karancin mai a fadin kasar nan, kuma da bukatar su farka domin shawo kan matsalar.
Ya ce, da farko lokacin da aka fara samun karancin Mai a lokacin damina a watan Oktoba, NMDPRA ta ce, an samu karancin Mai a Abuja da wasu jihohin arewa ne sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu; sai ya nuna cewa yanzu kuma da damina ta wuce babu wani dalilin cigaba da samun karancin Mai a sassan kasar nan.
Dan majalisar ya kara da cewa, “Rahotonnin sirri da ake samu daga jami’o’in tsaro na nuni da cewa da gangan dillalan sayar da Mai suke haifar da karancin mai din domin su yi zagon kasa ga kokarin gwamnati rarraba Mai a fadin kasar nan inda suka janyo karancin samun Mai din ta hanyar boye shi domin hakarsu ta cimma ruwa.
“Yayin da karancin Man ke kara ta’azzara wasu gidajen Mai suna sayar da man ne kan farashin da gwamnati ta gindaya, yayin da wasu gidajen mai masu zaman kansu kuma suke sayar da Man bisa farashin da suka ga dama.
“Mafiya yawan gidajen Man nan suna sayar da litar Mai sama da naira 300. Wannan abun kaito da damuwa ne ana wahalar da al’ummar kasa.”
Daga bisani dan majalisar ta ce, wannan barazanar da ke akwai, akwai bukatar gwamnati cikin hanzari da gaggawa ta dakile matsalar karancin mai tare da tabbatar da komai ya dawo yadda yake cikin kankanin lokaci.
Dan majalisar ya kuma ce, bisa karancin Mai da ake fama da shi da kuma hauhawar farashi da masu gidajen Mai ke kara tsauwalawa, abubuwan masarufi sun fara tsada kuma hakan ba cigaba bane ga al’ummar kasa.
Tun ma kafin wannan kiran na majalisar, a ranar Alhamis makon jiya hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bai wa masu ruwa da tsaki a harkar samar da Mai wa’adin kwanaki biyu da su gaggauta shawo kan matsalar karancin mai da ake fama da shi a kasar nan.
Sai dai kiran na DSS bai wani firgita masu gidajen Mai ba don har zuwa lokacin hada wannan rahoton a ranar Laraba wakilanmu sun tabbatar mana da cewar matsalar dai tana nan inda take inda jama’a ke kara shiga layi domin neman neman Mai kuma cikin farashi mai tsada.
Ita dai DSS ta ce, idan har wa’adin kwanaki biyu suka kare, suka kuma kama wani da yunkurin zagon kasa wajen samar da Mai a fadin kasar nan, za su daukeshi a matsayin mutumin da ke yi wa tsaron kasa zagon kasa kuma hukumomin tsaro ba za su kyaleshi ba.
Matakin na DSS na zuwa ne bayan wani ganawar da suka yi da jami’an kamfanin samar da Mai NNPC, da muhimman masu ruwa da tsaki a harkar samar da mai a fadin kasar nan, dillalai, masu mallakin defo-defo, direbobin tankokin dakon Mai, masu gidajen Mai masu zaman kansu.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan ganawar da suka yi a Abuja, Kakakin hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, ya ce, bayan mitin din da suka yin, kiran ya zama dole domin dakile aniyar wadanda suke haifar da matsalar karancin Mai a kasar nan haka siddan.
Afunanya ya ce, sun kira dukkanin masu ruwa da tsaki zuwa ganawar ne domin suna kallon matsalar na kokarin zama barazana ga tsaro, kuma tabbas da bukatar a gaggauta shawo kan matsalar karancin Mai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Kungiyar dalibai ta kasa da wasu kungiyoyin fafaren hula sun goyi bayan matakin da DSS din ta dauka, inda suka ce hakan ya yi daidai kuma za a samu natija wajen kawo karshen matsalar karancin mai a fadin kasar nan.
Ita kuma Hajiya Fatima Gambo daga jihar Kano ta shaida ma wakilinmu cewa, “Muna shan wahalar samun Mai gaskiya. Amma in ka lura kusan kowace watan Disamba zuwa farkon shekara ana samun karancin mai da wahalar samunsa. Amma duk da hakan ya kamata a ce an kawo karshen wannan matsalar domin al’umma na shan wahala.”
Ta kara da cewa, “Wasu lokutan ma sai mun gama bin layi muna jiran Man sai an kusa zuwa kanka sai a ce maka mai ya kare ko gidan Man sun tashi. Idan kuma kana sauri ko hanzari sai dai ka sayi mai tsada a wajen ‘yan bunburutu ko gidajen mai masu tsauwala farashi.”
Daga nan ta roki masu hannu a cikin lamarin da su ji tsoron Allah su daina kuntata wa jama’an kasa. Ta kuma yi fatan matsalar zai kawo karshe.
Shi ma wani direba mai suna Hamisu Alhaji Hamza da wakilinmu ya ci karo da shi a wani gidan mai na bin layi ya shaida cewar, “Abun dai ba a cewa komai. Amma muna fatan da wannan kiran na majalisa da wanda hukumar DSS suka yi, zai sanya masu sayar da man nan za su yi abun da ya dace su kawo karshen matsalar. Illolin da karancin mai je jawowa suna da yawa matuka,” a cewarsa.
Yanzu Haka harkokin na Neman tsaya cik a Kano Sakamakon karancin man fetur da ake fuskanta a kwanakin nan, kamar yadda Wakilinmu a Kano ya zaga wasu daga cikin gidan Sayar da man fetur din, ya lura da cewa da yawa wasu sunanda man a kasa amma saboda buri da aka dora akansa sakamakon hauhawar farashin da man fetur din keyi a halin yanzu yasa Suka Rufe gidajen Sayar da man domin amfani da irin wannan dama domin azurta kansu,
Wasu kalilan cikin gidajen da suke Sayar da man fetur din suna sayarwa ne akan farashin da ya Kama daga Naira dari uku har zuwa 350 Akan kowace liter guda, ya yin da ‘yan bunburutu ke cin karensu ba babbaka, inda ake Sayar da galan daya akan farashin Naira 1500.
Shugaban Kungiyar masu Sayar da albarkatun Man fetur Na Jihar Kano Alhaji Bashir Dan Malam ya bayyana cewa dalilin wahalar man fetur din da ake fama dashi a halin yanzu a Jihar Kano ya biyo Bayan yadda suke sayen man fetur din a hannun Kamfanoni masu zaman Kansu, su Kuma suna Kasa kayan nasu bisa farashin da suka ga zasu fita.
Wahalar man ya jawo da yawa aje ababan hawansu tare da zabar taka aayyadarsu domin Isa wuraren ayyukansu ko kasuwanninsu. Yanzu Haka a wasu gidajen man ana kwashe Kwana daya zuwa but Yu akan layi, ya yinda masu karamin karfi ke dandanar bakincin wasu masu Ido da kwalli da ake a bawa man adaidai lokacin da suka Isa gidajen man.