Karancin man fetur ya addabi Jihar Zamfara, wanda hakan ya haifar da tsadar rayuwa a Jihar yayin da ‘yan kasuwa ke korafin karancin man fetir da tsadar kayayyaki.
Leadership ta rawaito cewa yawancin mazauna jihar a yanzu suna tafiya mai nisa a kafa saboda ba za su iya biyan kudin ababen hawa ba.
- Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
- Wike: “Yakin Neman Zabe Ne Yanzu A Gaban Mu” – Rundunar Yakin Neman Zaben Atiku
Mallam Yunusa wanda ya zanta da manema labarai, ya ce isa birnin Gusau ne daga garin Danba mai tazarar kilomita bakwai da kafa.
“Na gargadi dukkan ‘yan uwana da kada su sake fitowa a 2023 da sunan zaben kowa saboda ban ga wata ribar dimokuradiyya a Nijeriya ba, musamman a Jihar Zamfara,” in ji shi.
Yunusa ya koka da cewa shi dan fansho ne yana karbar Naira 7,500 kacal a kowane wata daga gwamnatin jihar bayan ya yi wa gwamnatin jihar hidima tsawon shekaru 35 ba tare da wata kyautatawa ba.
“Yaya Nijeriya za ta gyaru yayin da masu hannu da shuni ke kara arziki yayin da talakawa ke kara talaucewa? Dimokuradiyya kenan? Kamar yadda ya tambaya.
Da aka tambaye shi game da sake fasalin kudin, sai ya ce, al’amuran masu wawure dukiyar Nijeriya ne, talakawa ba su damu da wannan batu ba saboda shugabannin sun san kansu.
A halin da ake ciki, a ziyarar da wakilinmu ya kai wasu manyan kasuwanni a Gusau, babban birnin jihar, ya gano cewa harkokin kasuwanci na tafiyar hawainiya ba tare da hada-hadar masu saye ba.
Galibin mazauna jihar sun kuma yi korafin cewa duk da karancin man fetur da ke ci gaba da addabar kasar, amma ga dukkan alamu Jihar Zamfara ce ta fi fama da matsalar kasancewar lamarin ya gurgunta duk wasu harkokin tattalin arzikin Jihar.
“Ta yaya gwamnatin jiha za ta yi ikirarin cewa tana gamsar da kowa yayin da jama’a a jihar ke mutuwa saboda yunwa,” kamar yadda ya koka.