A halin yanzu bangaren masu masana’antun kiwon kaji a Nijeriya da aka kiyasta ya kai na Dala fiye da Biliyan 4.2 na fuskantar gagarumar barazanar durkushewa musamman ganin masu gonakin kiwon kajin sun koka a kan karanci da tsadar masara da sauran kayyakin hada abincin kaji a sassan kasar nan.
Sashin bincike na jaridar LEADERSHIP Hausa ya gano cewa, bangaren kiwon kaji ke samar wa da Nijeriya akallla kashi 25 na kudin shigarta a bangaren harkar gona kuma gashi yana fuskantar tsananin barazanar ci gaba da wanzuwa.
Kungiyar masu kiwon kaji ta kasa (Poultry Association of Nigeria) ta nuna damuwarta musamman a kan yadda ake fuskantar karancin masara da kuma yadda farashin masarar ya yi ta tashin gwairon zabi, massara kuma ita ke a kan gaba na cikin ababben hada abinci kajin, wanda karancinsa ke neman durkusar da harkar kiwon kajin a kasar nan gaba daya. Masu harkar kiwon kajin sun bayyana cewa, wannan matsalar yana neman jefa ci gaban masa’anantun kiwon kaji cikin garari wanda hakan zai iya jefa ayyuka fiye da miliyan 25 cikin matsala.
Jardar LEADERSHIP Hausa ta kuma gano cewa, karancin marasa zai yi mummunan illa ga bangaren kiwon kaji musamman ganin masara ya kunshi akalla kashi 60 zuwa 70 na abincin kaji. Hakan kuma ya kai ga tashin gwauron zabi na farashin kwai da kaji saboda tsadar abincin kajin. Sun kuma bayyana cewa, a kwai tsananin bukatar a gaggauta kawo dauki ga bangaren masa’anantun kiwon kajin in ana son a ceto rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya da suka dogara wajen gudanar da harkokin rayuwarsu a bangaren kiwon kajin.
Tuni al’umma suke dandana sakamakon wannan tsadar kayayyakin, musamman abin da ya shafi kwai, inda a halin yanzu farashin kwai ya karu da kusan kashi 118.34, tun da shigo da masara daga kasashen waje ya yi kasa da kashi 97.91. Tashin farashin kwai abu ne da ya tayar wa al’umma da dama hankali musamman ganin kwai na daga cikin hanyar da ake samun sinadari ‘protien’ mai gida jiki, kulle gonakin kiwon kaji da dama da tashin farashin kayan hada abinci kajin, kamar masara da kuma yadda ake samun matsala a kokarin manoma na samun basuka daga cibiyoyin kudi ya matukar taimakawa wajen kara tsadar kwai a kasuwanni.
Wani mai kiwon kaji a Abuja kuma mamba a kungiyar masu kiwon kaji ta Nijeriya, Mista Sunday Akinola, ya bayyana abubuwan da suka hadu suka taimaka wajen kara tsadar kwai a kasar nan, sun kuma hada da yadda aka rufe gonakin kiwon kaji, wahalar da ake fuskanta wajen samun bashin gudanar da harkokin kiwon kajin daga bankuna, tsadar abubuwan hada abincin kajin, haka kuma rashin kyawun hanyoyin da suka nufa yawancin gonakin kaji a kasar nan sun taimaka wajen kawo cikas a samar da kwai duk kuwa da yadda ake bukatar kwan a fadin tarayyar kasar nan.
Mista Akinola ya kuma kara da cewa, bukatar da ake da shi na kwai ya zarce kwan da ake samarwa, kuma abin zai ci gaba da yin karanci ne a nan gaba, babu ranar da ake zaton kawo karshe wannan lamarin, rashin tabbas a harkokin canjin kudin kasashen waje zai kuma ci gaba da shafar harkar samar da kwai a watanni masu zuwa a nan gaba.
A bisa wadanna matsalolin da mamoma ke fuslanta, Mista Akinola ya nemi gwamnati ta gaggauta kawo tallafi. Ya nemki gwamnati ta sauwaka hanyoyin bayar da basuka ga manoman kaji, ya kuma karfafa samar da tsaro ga manoma don ci gaba da harkokin samar da kaji da kwai a Nijeriya.
A Jihar Kano, manoman kaji sun koka a kan tsadar abincin kaji a jihar, sun bayyana cewa daga farkon shekarar nan sun fuskanci karin fiye da kashi 340 na kudin abincin kaji a sassan jihar, sun kara da cewa, hakan ya matukar shafar harkokin su na kiwon kaji da samar da kwai abin da kuma tuni ya sa wasu gonakin suka rufe.
Binciken da aka yi kwanaki ya nuna cewa, yanzu ana sayar da abincin kaji a naira 8,000 zuwa N10,500, duk da ya danganata da kamfain da ke yin abincin don wasu sun fi wasu tsada.
A ta bakin shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta Jihar Kano, Umar Usman Kibiya, ya bayyana cewa, a halin yanzu wasu da dama daga cikin masu kiwon kaji a Jihar Kano na neman kulle harkar kiwon da suke yi saboda tsadar abinci kaji da masara.
Ya kara da cewa, “Gogoriyon neman masara daga kamfanonin flawa da masu yin abincin kaji da kuma masu cin masarar ya kara karanci da tsadar masarar a sassan Jihar.
Tsadar shigo da masara daga kasashen waje ya kara ta’azara matsalar da ake fuskanta. Yadda ake nwman masara ya kara farashinsa daga Naira N23,000 zuwa N33,000 kamar yadda muka samu bayani daga kasuwar ‘Dawanau International Grain Market’. Abin murna a nan shi ne yadda wasu kamfanoni suka bude rumbunan su, wannan hakan ya taimaka karya farashin da kuma wadatar masarar a sassan arewacin Nijeriya.”
Haka kuma kungiyar masu kiwon kaji na Jihar Delta ta nuna damuwarta na cewa a halin yanzu an kulle gonakin kaji fiye da 600 a yankin, kuma rashin isasun kayan kada abincin kajin kamar masara ne ya taimaka faruwar hakan.
Shugaban kungiyar na jihar, Miosta Eric Tomfawei, ya bayyana cewa, farashin masara ya karu da kashi 75, daga N225,000 zuwa N405,000 a kan Tan daya. Duk kuwa da wannan tsadar masu kiwon kaji sun kasa kara farashi saboda yadda aka samar da kwai da kaji brolas da yawan gaske.
Don tabbatar da magance wannan matsalar, Tomfawei ya nemi gwamnatin tarayya musamman ma’aikatar gona da albarkatun karkara su samar da masara daga runbuna boye hatsi ga masu kiwon kaji a farashi mai sauki.
Ya zargi wasu hukumomin gwamnati musamman Babban Bankin Nijeriya a kan yadda ta soke Tan 40,000 da aka shirya raba wa masu kiwon kaji wanda hakan ya taimaka wajen jefa masu kiwon kajin cikin hakin tsaka-mai-wuya, ya kuma nemi a kafa kwamitin bincike don gano yadda aka samu wannan matsalar. Ya kuma yi gargadi a kan cewa, yadda matasa ke rasa aiki a bangaren kiwon kaji a yankin zai iya haifar da tashin-tashina na matasa masu fafutukar ‘Niger Delta’. Wannan kuma koma bayan matsalar abinci da hakan ke haifarwa kenan. Don kaucewa durkushewar bangaren kiwon kaji a Nijeriya, Tomfawei ya nemi gwmanatin ta samar da tallafi na musamman ga masu kiwon kaji don kaucewa rikicin da bangaren zai iya shiga wanda zai kai ga Nijeriya ta fara dogara ga shigo da kaji da kwai daga kasashen waje wanda hakan za iyi matukar illa ga tattalin arzikin Nijeriya.
A nata tsokacin, wata kwararriya a bangaren ilimin abinci mai gina jiki, Deola Salami, ta bayyana cewa, tsadar kwai da saura abubuwan da ke samar da sinadarin protein kamar nama, kaji, kifi yasa sun fi karfin marasa karfi a Nijeriya, kuma kayyakin da ake samun wannan sinadarin kamar wake, waken soya sun fi karfin mai karamin karfi, a halin yanzu al’umma na ci gaba da cin abicin da basu gina jiki, wanda hakan yana da illa ga cikakkiyar lafiya da jin dadin al’ummar kasa.