ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Ake Noma Tan  Miliyan 12.4 Kacal Na Masara A Wasu Sassan Nijeriya -Shugaba

by Abubakar Abba
3 years ago
Masara

Shugaban kungiyar manoman masara na kasa Dakta Bello Abubakar Funtua ya bayyana cewa, Masara tan miliyan 12.4 kacal aka iya noma wa kasar, sakamakon matsalolin ambaliyar a wasu sassa na kudu maso-gabas da kuma arewa maso gabas na kasar nan.

Bello ya sanar da hakan ne a wani taron kwararru a fannin na noman Masara da aka gudanar a kwanan baya, inda ya kara da cewa, kazalika  karancin taki a wasu sassa na yankankunan,  ya kara janyo rashin nomanta kamar yadda ake bukata.

  • An Gurfanar Da Wani Mutum Da Ya Kashe Kaninsa Dan Shekara 6
  • Gwamnatin Jihar Gombe Na Bai Wa Fannin Noman Auduga  Mahimmanci – Kwamishina

“Tan miliyan 12.4 na Masara kacal aka iya noma wa a sakamakon matsalolin ambaliyar ruwa da karancin taki a wasu sassa na yankankunan kudu maso-gabas da kuma arewa ta gabas da arewa ta yamma.”

ADVERTISEMENT

Ya ci gaba da cewa, a yanzu Nijeriya na samar da Masara ninki goma ne kawai, inda ya kara da cewa, daga 1999 zuwa shekara ta 2019, a duk shekara masarar da ake nomawa a Nijeriya ta na ninkawa sau biyu.

A cewarsa, hakan ya sanya daga 2014 zuwa 2019 Nijeriya ta zama kasa ta biyu kan noman Masara a Afrika, inda take noma Masara tan miliyan 10.8 a duk shekara baya ga Afrika ta Kudu wadda take kan gaba a noman Masara a nahiyar Afrika, da take noma masara tan miliyan 12.9 a duk shekara.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Bello, ya yi bayyana cewa shekara ta 2014 Nijeriya ta noma Masara tan miliyan 10.1 inda a 2015 ta noma tan miliyan 11.6, sai a 2016 da ta noma tan miliyan 11.6, sai shekarar 2017 ta noma tan miliyan 10.4, a 2018 zuwa 2019 ta noma kimanin tan miliyan 11.0.

” Daga 2014 zuwa 2019 Nijeriya ta zama kasa ta biyu kan noman Masara a Afrika, inda take noma Masara tan miliyan 10.8 a duk shekara baya ga Afrika ta Kudu wadda take kan gaba a noman Masara a nahiyar Afrika, da take noma masara tan miliyan 12.9 a duk shekara.”

Bello ya kuma buga misali da cewa, a shekaru biyar na tsohowar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Nijeriya tana noma masara tan miliyan 10.8 a duk shekara.

Ya bayyana cewa, Masarar da Nijeriya ta noma a shekara ta 2019 tan miliyan 12.6 ta yi kasa idan aka yi la’akari da wadda ta noma a shekarar 2020 a sakamakon matsalar karancin ruwan sama,

“Masarar da Nijeriya ta noma a shekara ta 2019 tan miliyan 12.6 ta yi kasa idan aka yi la’akari da wadda ta noma a shekarar 2020 a sakamakon matsalar karancin ruwan sama. ”

A na sa jawabin Darakta Janar na Majalisar samar da iri ta kasa Dakta  Philip Ojo, ya nanata mahimmancin akan shuka ingantacce Irin Masara, musamman domin manomanta su samu riba mai yawa.

Ya ce, ya zuwa yanzu an samar da irin shuka na masara daban-daban har 140, don ganin an bunkasa  noman Masara  a Nijeriya .

” Akwai matukar mahimmancin akan shuka ingantacce Irin Masara, musamman domin manomanta su samu riba mai yawa. ”

Shi kuwa wani kwararre a fannin  Mista Joseph Kibaki ya bayyana cewa, akwai bukatar a samar da kyawawan tsare -tsare da shirye shirye, musamman daga bangaren gwamnatin tarayya domin a kara bunkasa fannin noman Masara a daukacin fadin kasar nan.

“Akwai  bukatar a samar da kyawawan tsare -tsare da shirye shirye, musamman daga bangaren gwamnatin tarayya domin a kara bunkasa fannin noman Masara a daukacin fadin kasar nan.”

Su kuwa wasu masana a fannin noman Masara a kasar nan sun bayyana wasu hanyoyin da ya dace a dauka domin a kara bunkasa noman Masara a kasar nan.

Sun sanar da hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a fannin suka gudanar tare da kuma kokarin lalubo da mafita kan kalubalen da fannin ke fuskanta.

Mahalarta taron sun kuma attaunawa kan kalubale da fannin ke fuskanta a kasar nan tare da kuma bayar da shawarwari, musamman ga gwamnatin tarayya kan yadda a lalubo da mafita akan kalubalen.

Masara
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Kasar Sweden Ta Yi Waje Rod Da Kasar Amurka A Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon Mata

Kasar Sweden Ta Yi Waje Rod Da Kasar Amurka A Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon Mata

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.