Yayin da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara suke kan dosowa, al’umman Nijeriya suna kan fuskantar karancin takardar kudi domin hada-hadar yau da gobe. Wasu mazauna Abuja da wasu jihohi da aka yi hira da su, sun koka kan wahalar samun takardar kudi da suke sha a fadin kasar nan.
Wannan kuwa na zuwa ne daidai lokacin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce sama da naira tiriliyan 3.87 aka fitar da su daga bankuna domin amfanin jama’a.
- CBN Ya Bayyana Shirin Kakaba Wa Bankuna Takunkumi
- Gwamnan Sakkwato Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2025 Na Biliyan 526
Bayanan na cewa kawo 93.34 na takardar kudin na hannun daidaikun mutane da ‘yan kasuwa, inda kuma sauran kaso 6.66 kacal ke yawo a tsakanin bankuna, inda jama’a kuma ke ci gaba da dogara da amfani da takardar kudin duk da inganta tsare-tsaren hada-hadar kudade ta yanar gizo.
An tattaro cewa ‘yan kasuwa musamman da suke karkara sun fi shan wahalar karancin takardar kudi, yayin da masu sayar da kayayyaki suka fi bukatar takardar kudi fiye da ta yanar gizo, kamar manoma a yankunan karkara, inda suke kin amincewa da hada-hadar yanar gizo kan danfara da suka yi ta fuskanta a baya.
Sakataren kungiyar masu POS a Nijeriya (APOSUN), Mista Isah Zakari, ya ce abubuwa da dama ne suka janyo karancin takardar kudi.
Yayin da yake daura alhalin hakan ga bankuna, inda ya ce tun daga watan Disamban 2023, bankuna suka rage ba su takardar kudi yadda suke bukata, sai dai suna zaban wasu su ba su da yawa.
Ya yi zargin cewa wuraren POS da dama mallakin wasu ma’aikatan banki ne, ya kara da cewa suna fitar da kudaden da za su rabar da kwastomominsu a wajen POS dinsu, yayin da saura kuma ke fama da rashin kudin.
Wasu bankuna a cikin Abuja suna da iyakan adadin kudin da suke iya bai wa mutane, hatta na ATM ma mutum ba zai iya cire kudi da yawa ba.
Masu POS din sun ce bankuna sun tilasta musu yanzu ba su da wasu mafita illa suke neman takardar kudi daga wajen ‘yan kasuwa ko gidajen mai, inda suka ce hakan ya sanya suka kara yawan kudin da suke cazan mutane.
Wani mai sana’ar hannu, Mista John Otafu, ya ce suna fuskantar wahala sosai wajen mu’amala da takardar kudi sakamakon karancinsa da rashin samunsa, yayin da ba su samun ko sisi a na’urorin ATM.
Wata mai sana’ar saida abinci, Titilayo Abayomi, ta ce, yanzu ta dauki dabarar boye takardar kudinta da kanta domin in ta ajiye a banki ba ta samunsu a lokacin da take so.