Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira biliyan 525.88 a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Juma’a.Â
Gwamnan wanda ya bayyana kasafin kudin a matsayin na ci gaba da gudanar da ayyukan raya jiha, ya bayyana alfanunsa a matsayin ci gaba mai dogon zango.
- Dalilan Da Suka Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci Duk Da Karuwar Kudin Shiga – Masana
- An Samu Rarrabuwa Kan Yunƙurin Barin Damagum A Matsayin Shugaban PDP Har Zuwa 2025
A kasafin, al’amuran yau da kullum sun samu Naira biliyan 176.3, yayin da za a aiwatar da manyan ayyuka da Naira biliyan 349.4 wato kashi 66 na kasafin.
Aliyu, ya bayyana cewar sha’anin ilimi zai samu kaso mafi yawa da kashi 25, yayin da sha’anin kiyon lafiya, aikin gona da ayyukan raya jiha za su biyo baya.
Gwamnan ya bayyana cewar kashi 44 zai tafi ne ga al’amuran yau da kullum wanda ya hada da sabon tsarin albashi Naira 70,000 ga ma’aikatan jiha da biyan fansho.
Aliyu, ya tabbatar wa ma’aikata cewar gwamnatinsa za ta fara biyan sabon albashin a watan Janairu 2025, ya kuma ce ba su karbi bashin ko Naira daga kowane banki ba, haka kuma ‘yan kwangila ba sa bin gwamnatinsa bashi.