Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki, ya gayyaci ministan lantarki, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta jasar (NERC) da su bayyana gabansa.
Kwamitin ya shirya wani zaman bincike da za a yi game da karin kudin wutar lantarkin da aka yi a baya-bayan nan.
- Mun Fara Raba ‘Yan Bindiga Da Makamai A Filato – Gwamna Muftaang
- Matsalar Tsaro: Amfani Da Fasahar Zamani Ya Wajaba Matuƙar Ana So A Yi Nasara – Gwamna Dauda
Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne, ya bayyana hakan yayin gudanar da ayyukan kwamitin.
Abaribe, ya ce majalisar dattawa ta sanya ranar 29 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a yi zaman, domin yi musu tambayoyi kan karancin wutar lantarki.
Ministan, ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi bangaren lantarki a Nijeriya da suka hada da rashin isassun kudi da rashin iskar gas.
Ya bukaci kwamitin da ya tallafa wa ma’aikatar lantarki domin cimma manufofinsa da kuma samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Sanata Abaribe ya kuma bayyana damuwa kan makudan kudin da ake zubawa a bangaren lantarki, masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokawa kan matsalolin da ake fuskanta.
Ya bukaci sanin bayanai kan abubuwan da ake haddasa karancin wutar lantarki da ake fama da shi sama da shekara guda a kasar nan.
Idan ba a manta ba tashar samar da wutar lantarki ta kasar ta sake faduwa a baya-bayan nan, lamarin da ya kawo adadin faduwar har zuwa sau shida cikin shekara daya.