Bayan da kotun sauraron karar shugaban kasa ta yi fatali da kararrakin da ‘yan takarar jam’iyyun adawa suka shigar a gabanta na kalubalantar nasarar Bola Ah-med Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a ran-ar 25 ga Fabrairu, yanzu haka ‘yan Nijeriya sun zuba ido su ga yadda za ta kaya a kotun koli.
Bai zo wa ‘yan Nijeriya da mamaki ba, lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi suka ki amincewa da hukuncin kotun sauraron karar shugaban kasa da ta zantar na tabbatar da nasarar Tinubu a zaben 2023.
A lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida dangane da hukuncin kotun a sakateri-yar jam’iyyar PDP a Abuja, Atiku ya bayyana cewa kasancewarsa dan gwag-warmayar siyasa a cikin rayuwasa zai ci gaba da fafatuka ba zai taba ja da baya ba.
A nasa bangaren da yake zantawa da manema labarai a Onitsha da ke Jihar Anambra, Obi ya ce ya bukaci lauyoyinsa su gaggauta kalubalen da ke cikin hukuncin kotun da alkalai biyar suka zantar karkashin shugabancin mai shari’a Simon Haruna Tsamani.
Yayin da Atiku ya ce yana mutunta hukuncin kotu, amma dai ya yi watsi da wan-nan hukunci. Ya lura cewa an gudanar da zaben bisa hanyar da bai kamata ba, wanda akwai bukatar bangaren shari’a ta samar da mafita.
Ya kara da cewa ya umurci lauyoyinsa su yi amfani da damar da tsarin mulki ya bayar domin ci gaba da kalubalantar shari’ar a kotun koli.
Haka shi Obi ya ce duk da yana girmama hukuncin kotu, amma bai amince da da-lilan da kotun ta bayar ba wajen zantar da hukunci.
“Dama ta ce a matsayina na dan takarar shugaban kasa da kuma manufar jam’iyyar LP in kalubalanci wannan hukunci ta hanyar daukaka kara cikin gagga-wa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa lokacin da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta zantar da hukunci a wani zama da ta yi na tsawon awa 12 a ranar Laraba da ta gabata, kotun karkashin jagorancin Tsammani ta tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a matsayin halartaccen shugaban kasa.
Ta ce kararrakin da jam’iyyu guda uku suka shigar bisa kalubalantar nasarar Tinubu, “Dukkanin kararrakin ba su da nagarta. Domin haka ta yi watsi da kararrakin.
“Wadannan kararraki ba su da nagarta. Na tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasan Nijeriya. Jam’iyyun sun gaza gamsar da kotun da kwararan hujjoji, domin haka wannan kotun ta zantar da hukuncinta na karshe.
Fusatattun jam’iyyun da ‘yan takaransu sun jaddada cewa ba a gudanar da zaben bisa ka’idojin da dokokin zabe da kundin tsarin mulki na shekarar 1999 suka shimfida ba.
Cikin kararrakin da aka gabatar a gaban kotu kan kalubalantar Tinubu sun hada da rashin samun kashi 25 na kuri’u a Babban Birnin Tarayya (Abuja). Haka kuma akwai rashin saka sakamaon zaben a na’ura da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba ta yi ba, wanda hakan suke ganin ya sa Tinubu ya samu nasara a zaben.
Haka kuma masu shigar da kara sun yi zargin an tafka magudi a zaben, wanda aka samu kuri’u fiye da kima da kuma bayar da cin hanci da rashawa a lokacin gudanar da zaben.
A cikin kararrakin, jam’iyyar APM ta bukaci kotun ta soke zaben shugaban kasa bisa dalilin zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa, wanda take ganin cewa bai kamata Shettima ya zama mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC ba, saboda yana rake da mukamin dan majalisar dattawa na Jihar Borno.
Kotun ta fara watsi ne da karar da jam’iyyar APM ta shigar na zaber Shettima a matsayin mataimaki. Jagoran kotun, mai shari’a Tsammani ya yi watsi da karar ne bisa rashin nagarta. Sannan ya ce INEC tana da hurumin kin saka sakamakon zaben a na’ura.
Bisa batun korafin rashin samun kashi 25 da Tinubu bai yi ba a Abuja kuwa, kotun ta ce Abuja daidai take da kowacce jiha, babu wata jiha da ta fi wata. Ta kuma yi watsi da batun karar da Atiku ya shigar na cewa Tinubu yana amfani da takardar shaidan dan kasa guda biyu.
Yayin da Shugaba Tinubu da magoya bayan jam’iyyarsa ke murna da hukuncin kotun, lamarin ya kasance mara dadi ga magoya bayan PDP da LP.
Duk da dai kundin tsarin mulki ya bai wa Atiku da Obi hurumin zuwa kotun koli, mutane da dama na ganin cewa bata lokaci ne su ci gaba da kalubalantar hukuncin kotun.
Dangane da abubuwan da suka wakana a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa, manazarta da daman a ganin cewa wace sabuwar shaida za su iya gabatarwa a kotun koli har su iya samun nasara.
Da yake tabbatar da dalilin da ya sa aka yi watsi da korar Obi, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Philip Okon ya ce, “Na ce karar da Obi ya shigar ba ta da nagarta. Idan ka yi ikirarin cewa ka samu kuri’u masu rinjaye, ya kamata ka bayyana adadin kuri’un da ka samu wanda ya sa ka yi nasara, sannan ka bayyana adadin kuri’un da abokan hamayyarka suka samu wanda ya sa suka yi rashin na-sara. Yana da sauki kamar A,B, C, D. Abin da Hope Uzodimma ya yi kenan a rikicin zaben gwamna.
“Ba za ku iya yin ikirarin cewa kun sami rinjayen kuri’u ba tare da gaya wa kotu adadin kuri’un da kuka samu da kuma rumfunan zabe da kuka samu kuri’u ba. Ba abu ne mai sauki a iya tabbatar da cewa kun ci zabe ba, domin abin da kotun sau-raren karar take nema kenanan, wanda rashin gamsar da ita har ya sa ta yi watsi da karar.”
Okon ya kara cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, ya kamata ‘yan Nijeriya su tashi tsaye don ganin an yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima wajen tabbatar an kammala shari’ar zabe kafin a rantsar da wadanda suka yi nasara.
A daidai lokacin da shari’ar ta dangana da kotun koli, ‘yan Nijeriya sun zuba ido domin ganin yadda masu shigar da kara za su iya gabatar da sabbin hujjoji da za su iya gamsar da kotu.