Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce za a yi wa ma’aikatan Nijeriya ƙarin albashi a wannan shekarar ta 2024.
Shugaban ya kara da cewa “za mu kara albashin kowanne ma’aikaci a Nijeriya, domin ƙarin shi ne abu mafi dacewa”
- Ba Za Mu Lamunci Lalaci Daga Waɗanda Aka Naɗa Muƙamai Ba– Tinubu
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
Da yake jawabin sabuwar shekara a jihar Legas shugaba Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an samar da ababen more rayuwa da kuma inganta tattalin arzikin ƙasar da zai kawo saukaka rayuwar ma’aikata da ‘yan Nijeriya.
“Gwamnatinmu za ta yi aiki tuƙuru domin tabbatar da mun taɓa rayuwar kowanne dan Nijeriya” inji shi.
Tinubu ya ce “Zuwa yanzu muna dab da kammala shirye-shiryen da muka kwashe watanni 7 da suka gabata na farfaɗo da tattalin arziki, domin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya baki daya.
Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci kan irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen ganin an inganta bangaren samar da wutar lantarki, duba cewa ba za a iya samun ci gaban da ake da bukata ba, ba tare da wutar lantarki ba.