Babbar Kotun Tarayya ta musanta cewa ta soke damar tsayawa takarar zababben gwamnan Jihar Abia, Dakta Alex Otti, wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar Labour Party kuma ya samu nasara zaben 2023.
Kotun ta ce, ita dai ta soke ‘yan takarar jam’iyyar LP na Kano ne wadanda suka yi takara a babban zaben 2023.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
- Labour Party Na Neman A Soke Zaben Ribas Saboda Sace Kayan Zabe Da Yi Wa Na’urar Zabe Kutse
Wakilinmu ya rawaito cewar tataburzar ta samo asali ne daga karar da Ibrahim Haruna, ya shigar a gaban kotun inda ya ke rokonta da ta soke tare da jingine dukkanin wani shaidar lashe zabe na dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar LP da aka ayyana sun yi nasara a zaben 2023 a jihar Kano da sauran jihohi 35 ciki har da babban birnin tarayya Abuja (FCT).
Biyo bayan tulin martani da suka biyo bayan hukuncin, Mai Shari’a Nasir Yunusa, ya ce, ‘yan takarar jam’iyyar na jihar Abia da suka shiga zaben 2023 ba su cikin wadanda aka shigar a karar.
Nasir Yunusa, ya ce, kotun ta soke zallar zaben fitar da gwani na LP a jihar Kano.
“Wannan kotun ba ta da hurumin bada wani oda na shaidar lashe zabe, su na da dama su nemi hakkinsu a kotun da ke da hurumi,” a cewarsa.
An dai bada rahoton cewa kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ayyana kuri’un da aka kada wa Alex Otti a matsayin kuri’un da aka yi asararsu, sai dai kotun ba ta yanke hukuncin soke shaidar lashe zaben da INEC ta bai wa Otti ba.
Mai Shari’a Yunusa ya ce, gaza tura jerin sunayen mambobin jam’iyyar LP ga INEC da ita jam’iyyar ta kasa ta yi kwanaki 30 kafin shirye-shiryen zaben fitar da gwaninta a hukuncinsa.
“Gazawar wanda ake kara na farko na mika sunayen mambobinta masu rijista a jihar Kano da Abia balo-balo ya saba da tanade-tanaden dokar zabe ta 2022 da sashe na 77(3), don haka zaben fitar da gwani na wacce ake kara na farko bai inganta ba, a hukuncin da Alkalin ya yanke a ranar Juma’a.