A halin da ake ciki yanzu haka, yanayin tattalin arzikin duniya na fuskantar guguwar rashin tabbas, a gabar da Amurka ke kara tsaurara matakan kakaba haraji kan hajojin da ake shigarwa kasar daga wasu kasashen duniya, matakan da masana tattalin arziki daga sassan kasa da kasa ke ta suka, tare da bayyana su a matsayin illa da ka iya dakile ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, baya ga ingiza hauhawar farashi, da gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa da hakan zai haifar.
Bisa halin da ake ciki, masu masana tattalin arziki na ganin matakan nan na kakaba karin haraji da Amurka ke aiwatarwa, za su ci gaba da zama barazana ga daidaiton tattalin arzikin duniya, kuma ko da kaso kadan daga cikin su Amurka ta aiwatar, hakan na iya tauye hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da haifar da hauhawar farashi a Amurka ita kanta.
- Sallah: ’Yansanda Sun Yi Alƙawarin Tabbatar Da Tsaro A Kano
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC
Idan mun duba irin wadannan matakai da Amurka ta dauka a baya, da wadanda take dauka a yanzu, ma iya cewa a wannan karo gwamnatin Amurka mai ci ta rungumi manufofi da tsare-tsare mafiya haifar da rashin tabbas sama da na kowane lokaci a baya, ta yadda lamarin ya zamo babban kalubale ga yanayin kasuwancin duniya.
Wani abun lura ma shi ne yadda gwamnatin Amurka take ta kokarin dorawa kasar Sin laifinta na gazawa, da koma bayan da take fuskanta ta fannin bunkasar tattalin arziki, zarge-zargen da ko shakka ba su da wata makama.
A daya hannun kuma, duk da cewa karin harajin na gwamnatin Amurka mai ci na iya rage gibin cinikayya tsakaninta da Sin, amma kuma hakan zai haifar da karuwar gibin cinikayya tsakanin Amurka da wasu karin kasashen duniya, wanda hakan zai sabbaba koma baya ga tattalin arzikin duniya baki daya.
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji.
La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani sabani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp