Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Festus Keyamo ya soki jam’iyyar PDP ta kasa bisa zargin da jam’iyyar tayi na cewar an sace wayar salular tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo a taron gangamin yakin neman zaben Jam’iyyar APC wanda ta gudanar a Abuja a makon da ya gabata.
Jaridar Daily Trust ce ta rahoto yadda aka sace wayar Namadi a taron da ya gudana a ranar Alhamis din da ta wuce.
A cikin wata sanarwa da Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi ikirarin cewa, satar wayar ta afku ne a yayin da ake kaddamar da tarihi kan rayuwar Marigayi tsohon gwamnan jihar Filato, Solomon Lar.
Sani ya ce, duk da samar da wadataccen tsaro a lokacin taron, amma wani ya kutsa a cikin taron, inda ya yi awon gaba da salular ta Namadi, inda Sanata Sani ya yi nuni da cewa, satar babbar abin kunya ce duk da irin wadataccen tsaro a gurin taron, amma aka yi awon gaba da salular.
Keyamo a martanin da ya mayar a shafinsa na Twitter ya ce, “Muna son mu ankarar da PDP cewa, babu wata wayar Salula da aka sace a lokacin da APC ta gudanar da gangaminta a jihar Legas ko kuma a yayin kaddamar da wani bangare na mata ‘ya’yan APC da ya gudana a Abuja.
A cewar Keyamo, APC ce ta aike Namadi Sambo jajen sace masa wayar salula a babban gangamin yakin neman zabe da PDP ta gudanar a Abuja a makon da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp