Yayin da ya rage kasa da wata biyu ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa mukalar da jaridar Daily Trust ta Lahadi ta yi ya nuna cewa bai cikawa ‘yan Nijeriya wasu alkawuran da yayi masu ba, lokacin da yake yakin neman zabe/ kamfe da suka hada da raba milyoyin ‘yan Nijeriya da fatara da kuma samar da ayyukan yi har milyan uku ko wace shekara.
Alkalumman da aka samu daga wurare daban- daban yawancin ‘yan Nijeriya sun rasa ayyukansu inda suka talauce a karkashin mulkin babbar jam’iyya mai mulki ta (APC) bama kamar idan aka yi la’akat kan yadda suke a shekarar 2015.
- Da Dumi-dumi: APC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Shehu Koko
- Gwamna Diri Ya Lashe Tikitin Tsayawa Takarar Gwamnan Bayelsa A Inuwar PDP
Sai dai kuma masu lura da yadda al’amura ke tafiya sun ce Shugabancin Muhammadu Buhari yakamata ace yayi fiye da zaton kowa na abubuwan da zasu bunkasa rayuwar Talakawa,amma sun ce rasa ayyukan yi kuncin rayuwa da fatara har yanzu Talaka na tare dasu a Nijeriya.
Sun ce abubuwa uku sun yi wa gwamnatin Buhari bazata da suka hada da fadin farashin man fetur tsakanin shekarar 2014 da 2017, wannan shi yasa kudin shiga suka ragu har aka shigo tabarbarewar kudaden shiga a 2016.
Ana cikin haka sai ga annobar cutar Korona ta shigo ita ma bata baro al’amuran koma bayan tattalin arziki ba, zuwa tayi tare dasu a shekarar 2020, 2021,wanda shine ya sake kara bayan tattalin arziki a duniya inda Nijeriya ta kasance ba saniyar ware bace.
Al’amarin ya hada da koma bayan tattalin arziki a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine da har yanzu shine ya zama kadangaren bakin tulu ma shugabannin kasashen duniya.
Daya daga cikin masu lura da yadda al’amura ke tafiya sun ce ba wata gwamnati da taba fuskantar matsalolin uku wannan na bin wannan a Nijeriya.
Ya kara jaddada cewa dukkan wadannan abubuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya ne da suka shafi duk kasashen duniya ba cikin suna so ba bama kamar nahiyar Afirka,inda yace Nijeriya ma tafi wasu kasashen a duniya karsashi matuka.
Masanin tattalin arziki Baffa Usman ya ce yayin da ana iya yafe ma gwamnati mai kammala wa’adinta saboda rashin rashin rashin cika wasu alkawuran data yi, amma ba a yafe mata ba saboda ta kasa yin abinda yafi wadanda ta tarar.
“Shugaban ya samu duk abubuwan da suna iya taimaka ma shi yayi wasu sauye- sauyen da zasu za suyi babban tasiri,amma yayi tunanin kamar shekaru takwas ba za su kare bane.
“Da farko ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya samu wadanda zasu taimaka ma shi tafiyar da ayyukansa da manufofi, wani abu daban daukar laokaci kafin ya samu kwamitin tattalin arziki da ya san abinda yake.Kana iya tunawa wai sun ce sun samarda ayyuka ta hanyar ta kafar sadarwa ta zamani a dukkan kananan hukumomi 774 na kasa.Wannan zumar da aka lasa ma wasu a baki tuni ta koma madaci, koda – yake sun ba wasu ‘yan kalilan wata garabasa kamar yadda Usman ya bayyana”.
Karuwar rashin ayyukan yi sai suna iya karuwa nan gaba kadan za a sani ko gane adadinsu cikin wasu ‘yan watanni masu zuwa aikin yi.
“An yi ma tattalin arziki gyambon da zai dade bai warke ba bama kamar tsarin ‘cashless policy’ wanda a zarihi kana hada- hadar kudade ta kafar sadarwa ta zamani kai ma ka san da hakan ne,sai dai a badini babu ko sisin kwabo ko anini a hannunka,gwamnatin Buhari ce ta tilasta yin tsarin.Milyoyin kananan ‘yan kasuwa da suke da kasa da Naira 20,000 yanzu tamkar basu a doron kasa ne domin kuwa sun zama mabarata/ rabbana ka wadata mu”.
Manufar Buhari Nijeriya Ta Zama Ingantattar Kasa
Daya dga cikin manyan alkawuran kamfen da Shugaban kasa yayi ma ‘yan Nijeriya a shekarar 2015 shine yayi maganin rashin aikin yi da fatara wadda ta addabi mutane a kasa, ta hanyar samar da ayyukan yi da suka kai milyan uku ko wace shekara.
Da ace ya cimma wannan burin Shugaban kasa zai bada ayyuka milyan 24 zuwa yanzun.
Amma idan aka duba da alkalumman wadanda basu da aikin yi a kasa wannan ba tare da wani abin gamsarwa ba ya nuna gwamnati ta gaza cika manyan alkawuran da tayi ma ‘yan Nijeriya.
A jawabin da yayi bayan da aka kaddamar da shi a shekarar 2015,Shugaban kasa yace “Rashhin aikin yi musamman ma, a tsakanin matasa shine babban abinda yake cikin manufofinmu.Mun yi shirin haka ne wajen farfado da aikin noma, ma’adinai, da kuma tononsu,bigu da kari har ma da bada bashi ga matsakaita da kananan ‘yan kasuwa domin taimaka masu su fara harkokin kasuwanci.”
A manufofinsu na kamfen kafin su kada tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da ita jam’iyya mai mulki a lokacin (PDP) jam’iyyar APC tana da abubuwa da yawa na cigaba da take son yi ma ‘yan Nijeriya, daga cikinsu akwai tsarin rage radadin fatara,fatattakar rashin tsaro, kara inganta samar da ayyukan yi,inganta tattalin arziki,tareda yaki da karbar rashawa da cin hanci.
Alal misali lokaci sakon kirsimati ga ‘yan Nijeriya a watan Disamba 2014,Lai Mohammed,wanda, a lokacin shine sakataren wayar da kan jama’ na kasa na jam’iyyar APC yanzu shine Minista yada labarai da al’adu yace, “Alkawuransu takwas don inganta Nijeriya,wadanda suke daga cikin manufofinmu abinda yana tsakaninmu ne da ‘yan Nijeriya.Shekara ta farko mun yi alkawarin zamu bada ayyuka milyan uku ta hanyar tsare- tsaren ayyukan al’umma da kuma mau da shi tsarin tattalin arziki zuwa yadda kowa zai bada tasa gudunmawa wannan shine manufarmu.
“Zamu kara inganta al’amarin tsaro ta hanyar daukar jami’an tsaro a kalla100, 000 na jami’an ‘yansanda da kuma kafa wasu jami’an tsaro yadda ya dace da za a basu kayan aiki isassu da zasu yaki ‘yan kungiyar Boko Haram da kuma duk wani al’amarin da yayi kama da ta’addanci.Hakanan ma za a kara masu albashi da ingantattun sharuddan aikinsu da zasu sa su maida hankalinsu ga aikinsu na tsaro.
“Wajen yaki da rashawa da cin-hanci a’amarin daya karade al’amura da yawa na rayuwa,za a fuskanci al’amarin shi ba sani ba sabo, ma’aikata wadanda basu da da’ar aiki suka sa kansu ciki za a kore su daga aiki, ko daukar tsauraran matakai kansu da suka hada da zama gidan Kurkuku.
“Domin sake inganta matasanmu domin samun ayyuka masu nagarta zamu taimaka masu da bashin da baya da ruwa ga daliban da suke jami’oi da makarantun fasaha wadanda suka cika sharuddan karatun,za a samar da bashin ne ta Bankuna ta hanyar amfani da ruwan za mu bullo da tsarin ciyar da yara ‘yan makarantar Firamare kyauta.
“A karo na farko na yaki da fatara za a fara gabatar da tsarin bada taimakon kudade na wata- wata ga ‘yan Nijeriya milyan 25 da suka fi kowa talauci.”
Wakilinmu ya bada rahoton da ke nuna yayin da ake ganin an murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram, a sashen Arewa ta gabas,akwai sabon tashin hankali na kungiyar masu faftukar neman ‘yanci da kasar Biyafara (IPOB) a sashen Kudu maso gabas, ga cigaba da sace- sacen albarkatun man fetur a Kudu maso Kudu wanda ya kawo cikas ga kudaden shigar da Nijeriya yakamata ta samu.ga kuma garkuwa da jama’a. a sashen Arewa maso yamma,duk wadannan sun maida nasarorin da aka samu ta bangaren tsaro kamar ba a samu ba.
Koda yake duk irin wadannan matsalolin an sha akan wasu a hankali a watannin da suka gabata manudar Shugaban kasa Buhari ta inganta aikin gona shi ma wannan na fuskantar matsala domin kuwa manoma da yawa babu yadda za ayi su shiga gonarsu saboda dalilan da suka shafi tsaro.
Yawan Marasa Aikin Yi
Binciken da jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi ta yi ya nuna cewa yawan marasa aikin yi a watannin Afrilu zuwa Yuni na kawata ta biyu Afrilu zuwa Yuni 2015 lokacin da Buhari ya hau kan karagar mulki Buhari kashi 14.9 cikin 100 da ya bada mutane milyan 6.1da dubu dari daya kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar da bayani ya zuwa shekarar 2023,alkalumman rashin aikin yi sun ninka sau uku,kamar dai yadda hukumar ta ce ya kai kashi 33.3 cikin 100, wanda shi yake nuna kusan mutane milyan 23.18 da dubu dari da tamnin na ‘yan Nijeriya.
Duk da yake alkalumman karshe da aka fitar ta hanyar hukumar kididdiga ta kasa a karshen watanni uku na shekarar 2020 ko abinda mutane suka fi sani da kwata ta karshe a shekarar na rashin aikin yi ga ‘yan Nijeriya abin ya zarce milyan 23.
Kamar yadda hukumar ta harkokin kididdiga ta kasa NBS,al’amarin daya shafi rashin aikin yi tsakanin mutane masu shekarat 15 zuwa 64,da suke son yin aiki za kuma su iya yi ba tare da la’akarin ko suna da ayyukan yi hannunsu.
Yadda aka bayyana alkalumman na wadanda basu da aikin yi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi ta nuna a kwata ta biyu ko Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2015,rashin akin yi tsakanin mutane masu shekaru tsakanin 18 zuwa 64 wannan na da kashi 14.9 yayi da abin yayi sama zuwa kashi 17.8 kwata ta uku watannin Yuli zuwa Satumba.
A shekarar 2016, rashin aikin yi kashi 12.9 a kwata ta farko watannin Janairu zuwa Maris,kashi 13.3 a kwata ta biyu Afrilu zuwaYuni,kwata ta uku Yuli zuwa Satumba kashi13.9,yayin da kwata ta hudu Oktoba zuwa Disamba kashi 14.2.
A shekarar 2017 alkalumma sun nuna a kwata ta farko watannin Janairu zuwa Maris kashi 14.4 ita kwata ta biyu kashi 16.2 ne;kwata ta uku nada kashi 18.8 yayin da kashi 20.4 na kwata ta hudu ne.
Hakanan ma a shekarar 2018 alkalumma sun nuna kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta fitar ya nuna kashi 21.8 na kwata ta farko ke nan,kwata ta biyu tana da kashi 23.1,yayin da kwata ta uku na da kashi 23.A kwata ta hudu ba a fitar da alkalumman rashin aikin yi ba hakanan ma gaba dayan shekarar 2019 da kuma kwatar farko ta 2020 har sai kwata ta biyu inda alkalumma suka nuna 27.1da kwata hudu ta 2020 inda abin ya fi daure kai da kashi 33.3.
Ministan kwadago Chris Ngige lokacin da yake kare mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ya bada ayyukan yi milyan bakwai tun lokacin daya fara mulki a shekarar 2015,ta hanyar tsarin zuba jari ta tsare-tsaren tallafawa al’umma (SIP),tsarin N-Power da aka fara shekarar 2016.Tsarin shine daya daga cikin alkawurran yakin neman zabe ta jam’iyyar APC tayi wa mutane.
Tsarin an raba shi gida hudu da farko akwai ciyar da ‘yan makarantun Firamare na gwamnati abinci; sai kudaden da ake ba ‘yan Nijeriya marasa galihu, sai tsarin N-Power ga wadanda suka kammala jami’oi basu da aiki,sai tsarin,akwai kuma tsarin tallafawa mata ‘yan kasuwa,masu sana’ar hannu, da ‘yankasuwa.
Duk da haka alkalumma da hukumar kididdiga ta kasa akan samar da ayyuka a kwata ta biyu a shekarar 2015 an samar da ayyuka 141,368,kusa da lokacin da Shugaba kasa Muhammafdu Buhari zai hau kan karagar mulki, an samar da ayyukan yi da suka kai 475,180 a kwata ta uku na 2015,gaba daya jimlar ayyukan da aka samar sun kai 499,521.
A kwata ta farko a shekarar 2016 an samar da ayyukann yi da suka kai 79,469.A kwata ta biyun an samar da155, 444.Kwata ta 3 ta shekarar 2016 an samar da 187,226.Wannan shi yasa gaba daya an samar da ayyukan da suka kai 1,538, 2008 a kwata ta uku a shekarar 2016, sai dai babu wani bayani daga hukumar dangane da kwatar karshe ta 2016 da ta farko ta shekarar 2017.
Wannan shi ya kawo karshen maganar da Ministan kwadago yace sun samar da ayyuka milyan bakwai tun shekarar 2015, al’amarin da sam ba yadda za ayi ta yiyu.
Hanyar da ake bi kamar yadda hukumar kididdiga ta bada sun hada da aiki kai tsaye, mai zaman kanshi, da kuma gwamnati.
Maganar da Minista yayi inda ya ce gwamnatin tarayya ta samar da ayyuka milyan bakwai ta hanyar N-power wannan ba gaskiya bane domin kuwa shi tsarin ya ba mutane 500,000 aiki ne, bayan da shi Ngige yayi ba yadda za a tabbatar da hakan idan aka yi la’akari da alkalumman da hukumar kididdiga ta bayar da halin da ake ciki na tattalin arziki.
Yawan karuwar fatara
Ta al’amarin daya shafi kawar da fatara Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin zai raba ‘yan Nijeriya milyan 100 daga fatara cikin shekara 10, haka nan ma a watanYuni 2021 ya kara tabbatar da niyyar gwamnatinsa na cika alkawarin.
A watan Yuni na shekarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin mai suna kwamitin kasa na kawar da fatara wanda an yi shirin zai fidda ‘yan Nijeriya milyan 100 daga fatara kamar yadda yayi alkawari.
Da yake kara jaddada niyyar ta Shugaban kasa ya cika alkawarinsa mai bashi shawara ta musamman a harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma Malam Garba Shehu,a wata sanarwar daya fitar a Yuli 2021 inda yace,”Ina son in kkara jaddadawa ‘uan Nijeriya cewa yana tabbacin ana iya samun nasarar fitar da ‘yan Nijeriya milyan 100 daga fatara”.
“Kasar Nijeriya Allah ya albarka ce ta da yanayi mai kyau da kasa maikyau ga kuma al’umma da kayayyakin aiki da tare za su iya nunawa da akwai bambanci domin hazikan matasa da ake dasu.
“Zamu iya yi za kuma mu yi babu wata dama da za a tsaya kanal’amari daya bayan duk mun san matsalolin da muke fuskanta wajen samar da man fetur ga yadda farashin shi yake daduwa da tashi a kasuwar mai ta duniya, bayan muna da hanyoyin da zamu noma kayan amfanin gona da kiwon dabbobi.
Amma hukumar kula da kidigga ta kasa ta bada sanarwar Nijeriya tana da mutane milyan 133 wanda shi ne kashi 62.9 da suke cikin fatara mai tsanani.
Wannan kamar yadda hukumar tace mutane milya 133 ‘yan Nijeriya sun saba da kasancewa suna fuskantar rashin fiye da wani abu ko al’amari daya ko kuma daga cikin a kalla kashi 26 na abubuwan da suka rasa,sai dai abu mafi dacewa ace sun same su. Hudu daga cikin kowadanne ‘yan Nijeriya 10 sun saba da rashin kudi,haka nan ma 6 daga cikin 10 su sun riga sun daura aure da talauci ko fatara.
Rashin samun abubuwa tsakanin matsakaitan matalauta ya nuna irin yadda fatara take da tsauri saboda mizanin ya wuce kashi 40.9.Kamar yadda matalauta wajen sabawa da rashin samun wani abu ko abubuwa ko dai akalla rabi na abinda ake auna fatarar da su da ke nuna abin ya kai ga wata kasaita.
Akwai wasu wurare da suke da matalauta da yawainda ko wane mutum ya rasa kashi 51 na abubuwan da ake gwaji dasu masu nuna al’amarin ya kai intaha,misali Kebbi ta Kudu da kuma Bayelsa ta yamma kamar yadda hukumar kididdigar ta bayyana
Ya kara jaddada “Bakwai daga cikin ‘yan Nijeriya suna zama ne a kauyuka kuma matalauta ne idan aka kwatantasu da hudu daga cikin 10 da suke zama a birane.An fi samun matalauta a kauyuka inda kashi 72.0 suke matalauta marasa abin hannunsu, idan aka yi la’akari da kashi 42.0 na mutanen da suke zama a birane.A takaice ko kididdige kashi 70 na ‘yan Nijeriya suna zama ne a kauyuka duk da haka an san gida ne na kashi 80 na mutanen da suke Talakawa.
Karin kasancewar fatarar abin ya fi kamari a kauyuka da kashi 41.9 idan aka gwada da wadanda ake da su a birane da suke kashi 36.9.
Bankin duniya yace yawn ‘yan Nijeriya da suke cikin fatara abin ya kai zuwa milyan 95.1 a 2022.
Bankin ya bayyana hakan ne a wani rahoton daya fitar na binciken da yayi kan fatara mai taken “Ana sa ran ‘yan Nijeriya za su maida komada a shekara ta: 2022 bincike kan halin fatarar da ake ciki a Nijeriya.”
Rahoton bai manta da na yadda ‘yan Nijeriya suka kar bin sahun talauci sanadiyar bullar annobar cutar Korona domin fiye da milyan 5 suka shiga cikin fatara a 2022.
Da yake kudaden da suke shigowa mutane sun ja baya a suk wani bangare na tafiyar da rayuwa a shekarar 2020, Bankin ya kara bayani na an yi hasashen fatara ko talauci su kara addanar Talakawa, yayin da kuma wasu Magidanta da suka fara bankwana da fatara bada dadewa ba kafin Korona suna iya komawa ruwa.
“Wuraren da ba a tsammanin al’amarin zai iya tasiri wani abu daban na iya tasowa),sai dai tunanin da ake zai yi matukar wuya al’amarin fatara ya sauya domin akwai mutanen da tuni sun kama hanyar talaucewar daga milyan 82.9 a shekaru 2018/19 zuwa milyan 85.2 a 2020 da kuma milyan 90.0 a shekarar 2022, wannan ba komai ya jawo haka ba sai karuwar yawan mutane wanda kuma al’amari ne daga Allah.
Hakanan ma gwamnatin tarayya da Kanata tana kasafin kudin daya kai Naira bilyan 500 ko wace shekara saboda tsare- tsaren zuba jari inda za a saukakawa al’umma.
Masana sun ce ba wani siddabarun da za ayi kan magance matsalar rashin ayyukan yi, da fatara a cikin wata biyu.
Wani masani kan harkokin cigaba kuma shugaban kungiya mai zaman kanta da ake kira da suna Cibiyar son kamanta gaskiya Umar Yakubu,yace da wuya alkawarin da Shugaban kasa ya yi ya cika shi na al’amuran da suka shafi fatara da rashin aikin yi,ganin wata biyu ne suka rage ma shi ya kammala wa’adinsa na mulki.
“Lokacin da Shugaban kasa ya hau karagar mulki daya daga cikin abubuwan da yace shine zai fitar da ‘yan Nijeriya milyan 100 daga fatara bayan yanzu al’amarin fatara al’amarin ya fi shurin masaki,inda mutane da yawa kara talaucewa suke yi.
“A wata biyu masu zuwa ba wani siddabarun da za a iya yi na kara inganta al’amuran fatara da rashin ayyukan yi
Yakubu yace idan ana son magani su matsalolin biyu sai Nijeriya ta gyara al’amarin wutar lantarki, abubuwan more rayuwa,rage shigo da kaya daga kasashen waje,maganin tabarbarewar tsaro,saboda hakan zai ja hankalin masu zuba jari.
“Yanzu ana kashe bilyoyin daloli kan wutar lantarki sai dai wani abu kuma da kyar muke iya samun mrawatts 5,000 megawatts,domin hakan ba wani taimakawa zai ba na bunkasa harkar masana’antu, musamman ma bangaren aikin noma, yin wadansu kayayyaki, karafa, da dai sauransu.
“Haka ma kudaden da ake kashewa wajen shiro da kaya sun yi yawa domin hakan yana durkusar da kokarin da muke yi a gida.Duk da yake akwai cigaban da aka samu ta bangaren noma, har yanzu muna shigo da yawancin abubuwan da zamuiya yin su a gida. Gwamnati mai hawan mulki badadadewa ba dole ta kalli al’amarin shigo da kaya daga waje.
“Al’amarin samun rance daga Bankuna cikin sauki yana da amfani sai dai abinda ke faruwa yanzu shi ne Bankuna suna kara ruwa na ribar da suke cirewa domin kashi 27 cikin 100 na bashin da aka amsa manya,matsakaita ,da kananan masana’antu zai masu wuya su ji dadin tafiyar da al’amura.
Daga karshe al’amarin tsaro shi ma wani al’amari ne mai muhimmanci domin babu wani mai zuba jari zai so ya zo wurin da harkar da zai yi bata da tabbas,wajen la’akari da yadda wurin yake,wannan shi zai iya shafar samarwa matasa da ayyukan yi.
“Idan aka yi la’akari da duk matsalolin da aka yi bayani zai yi ma Shugaban kasa wuya daukar wanui mataki ko wanu abu,cikin wata biyu da suka rage.
Fadar Shugaban kasa tace ba wasu sabbin abubuwa ake magana ba
Da ta ke maida martani fadar Shugaban kasa tace wannan rahoton ba bakon al’amari bane saboda kuwa babbar jam’iyyar PDP ta fuskancin irin hakan lokacin da take mulki.
Babban mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa shawara na musamman Malam Garba Shehu,cewa yayi jam’iyyar PDP ma ta yi fama da irin wadannan matsalolin, ba bakin abubuwa kuka kawo ba.”
Kafin dai ya maida martanin Jaridar Daily Trust ranar Lahadi ce ta aika da wasu tambayoyi inda tace wani rahoton da aka yi bincike ya nuan Shugaban kasa Muhammadu Buhar bai cika alkawuran kamfen da ya yi ma ‘yan Nijeriya kamar yadda ya kamata ba, a kan rage fatara da rashin ayyukan yi, yayin daya rage ma shi wata biyu kacal ya kamma wa’adin mulkinsa.