- Za A Kashe Wa Kowane Dan Nijeriya Naira 538 Kullum
- ‘Yan Majalisar Tarayya Za Su Sha Romon Dimokuradiyya Da Naira Biliyan 127,769
A farkon makon nan ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kudirin dokar kasafin kudin 2024, na Naira Tiriliyan 28.77 wanda ya kunshi karin Naira Tiriliyan 1.2 da majalisa ta yi a kan abin da shugaban kasar ya gabatar mata da farko.
Kasafin na 2024 wanda kwata-kwata bai wuce wata guda ba tsakanin gabatar da shi da kare shi da kuma rattaba masa hannu, zai fara aiki ne nan take bisa amincewa da kuma rattaba hannu a kai daga bangaren zartaswa. Inda hakan har ila yau, ya cika burin gwamnati mai ci ta Tinubu na aiki da sabon kasafi a tsakanin Janairu zuwa Disamba.
- Sin Ta Sha Alwashin Hadin Gwiwa Da Sauran Sassa Wajen Dakile Tashin Hankali A Tekun Red Sea
- Tsohuwar Ministar Jin Kai, Sadiya Ba Ta Ƙi Amsa Gayyatarmu Ba – EFCC
A jawabinsa ga manema labarai, shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan kasafin kudi, Sanata, Solomon Adeola Olamilekan ya ce, majalisa ta 10 za ta bayar da goyon bayan ganin ana ci gaba da gudanar da kasafin kudi a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.
Sai dai majalisar ta koka da yadda aka kawo mata kasafin a makare tare da jaddada kiran a rika gabatarwa tun ana sauran wata uku shekara ta kare kamar yadda doka ta tanada, wannan ne zai bayar da damar a yi aiki a kan bayanan kasafin a tsanake.
Daga wasu abubuwa da aka lura da su a kasafin, an cire wasu ma’aikatu daga jerin wadanda za su amfana da tallafin kudi daga gwamnatin tarayya tare da umurtar su, da su kara kaimi wajen samar da hanyoyin kudaden shiga tare da ware wa gwamnatin tarayya nata kason daga abin da suka tattara.
A kasafin kudin na 2024, an ware Naira Tiriliyan 8.27 don biyan bashin da gwamnati ta ciwo daga kasashen waje. Kana sashen shari’a ya samu kaso mai tsoka na Naira Biliyan 341.62 yayin da bangaren ilimi a matakin farko (UBEC) ya samu Naira Biliyan 263.044.
Daga cikin kasafin, majalisar wakilai za ta sha romon dimokuradiyya da Naira Biliyan 78.624 yayin da majalisar dattawa za ta bararraje da Naira Biliyan 49.145; baya ga Naira biliyan 36.727 da aka ware na tafiyar da ayyukan majalisun na tarayya.
Bangaren tsaro dai shi ne ya fi kowanne samun tagomashi da Naira Tiriliyan 1.308, sai ma’iakatar ayyuka da aka ba ta Naira Biliyan 892.46, ma’aikatar ‘yansanda kuma Naira Biliyan 869.121, yayin da Ilimi ya samu Naira Biliyan 857.134.
Sauran sassan da ake ganin sun dan samu kaso mai dan gwabi sun hada da kiwon lafiya da walwalar al’umma Naira Biliyan 667.577, ma’aikatar cikin gida Naira Biliyan 362.552; ma’aikatar matasa Naira Biliyan 201.467; kana Ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro ya samu naira biliyan 199.763.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan kasafin kudi, Hon. Abubakar Kabir Bichi ya bayyana cewa, sun yi la’akari da kudin shigar da gwamnatin tarayya za ta tara da kuma kokarin daidaita farashin Dala a kan Naira da kuma hauhawar farashin kudin kasashen waje, wanda ba shi da tabbas yayin amincewa da kasafin.
…Fashin Bakin Farfesan Tattalin Arziki A Kan Kasafin Na Tarayya Da Jihohi
Farfesa Ahmad Sanda, shehin malami kuma masani a bangaren tattalin arziki (Economy) da ke koyarwa a Jami’ar Usmanu Danfodio ta Sokoto, ya ce, akwai bukatar gwamnatin kasar nan, ta sanya lura da hankali wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsaren da ke cikin kasafin kudin 2024 lura da tulin matsalolin da suke jibge a kan kasar.
Ya ce duk da kasafin kudin na Naira tiriliyan 28.7 da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu a kwanakin baya ba zai taka kara ya karya ba idan aka duba tulin matsalolin da suke akwai musamman na hauhawar farashin kayayyakin bukatu, amma gwamnati za ta cimma nasarar sanya kasafin ya yi tasiri ga tattalin arziki ne kawai idan ta tabbatar da gudanar da abubuwan da aka tsara a cikin shekarar nan kuma a bayar da kudaden aiwatar da ayyukan a kan lokaci.
Ya ce, tun shekarar 2016 da ‘yan majalisa suka shafe tsawon watanni bakwai ba tare da amincewa da kasafin kudin ba, an yi kokari wurin samun daidaito daga kasafin 2018 ta za a rika amincewa da shi kafin a shiga shekararsa. Kuma har zuwa yanzu ba a samu dogon tsaiko wajen amincewa da kasafin daga majalisar kasa ba.
Farfesa Ahmad Sanda ya kuma shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, “Idan aka kwatanta wannan kasafin da shekarar da ta gabata an samu kari na kaso 15.9 wasu za su iya cewa wannan ya nuna alamun za a samu karin tagomashin farfado da tattalin arziki domin an samu kari a kasafin na bana.
“Idan ka duba bangaren biyan bashi kawai na gwamnati; gwamnati ta kebe tiriliyan 8.2 domin biya, ka ga kenan bangaren gudanar da manyan ayyuka ya samu tiriliyan 9.9, yayin da kuma bangaren ayyukan yau da kullum aka ware masa tiriliyan 8.7.
“Idan aka tattaro dukkanin kasafin gwamnatin tarayya da na jihohi baki daya idan aka hada zai kai tiriliyan 44.9 ne. Sannan, idan aka duba yawan mutanen Nijeriya da muke da fiye da miliyan 200 to a zahirin gaskiya wannan kudin bai taka kara ya karya ba idan ka duba bukatun ‘yan Nijeriya, saboda kasafin 2024 na tiriliyan 44.9 na gwamnatin tarayya da dukkanin jihohi 36 zai kama za a kashe naira 538 ga kowani dan Nijeriya a kowace rana.
“Ka duba farashin kaya a halin yanzu meye naira 538 zai yi wa dan Nijeriya a kowace rana? Idan ka duba kudin za a ga kudi ne mai yawa, amma ka duba tulin abubuwan da ke gaban kasar musamman yawan jama’a sai ka ga wannan kudin ba wani abu ba ne da ya taka kara ya karya.”
Don haka ne, Farfesan kai tsaye ya ce, ka da ‘yan Nijeriya su dogara da wannan kasafin kudin da tunanin wai zai kawo wani gagarumin sauyi ga tattalin arzikin kasa ba.
Sai dai ya ce, akwai babbar dabara da in gwamnati ta yi wannan kasafin zai yi zarra wajen bunkasa tattalin arziki da habaka kasar.
“Da gwamnati za ta tabbatar abun da ta ware wa harkar tsaro za a bi hanyoyin da suka dace kudin ya je inda aka ware kuma a tabbatar ya yi amfani to ka ga manoma za su samu kwanciyar hankali su yi noma sosai; ta wannan bangaren za a iya cewa kasafin zai taimaka sosai wa tattalin arziki.”
A gefe guda, da yake tsokaci kan naira tiriliyan takwas da aka ware cikin kasafin domin biyan basuka, ya ce, koda an biya basukan za kuma a iya sake ciyo wani bashin, manufar ita ce ana biyan basuka kuma ana ciyo wasu sabbi.
“Idan aka duba wasu bayanan da gwamnati ta yi, ta nuna cewa za ta tabbatar an kara kudin shiga ta hanyar tabbatar da masu biyan haraji suna biya kuma an tabbatar kudin ya shiga cikin aljihun gwamnati, idan aka yi haka to ana sa ran ciwo bashi zai ragu. Amma kar mu yi tunanin gwamnati za ta daina ciwo ba shi, wannan kusan ya zama kusan kowani kasafi za a ware biyan basuka kuma za a ciwo wasu.”
Farfesa Ahmad Sanda ya ce, nasarar kowani bangare ya danganta da isar kudin da aka ware da kuma tabbatar da an bi abubuwan da aka zana a kasafin ne, domin babbar matsalar da ake samu ita ce tsaiko na fitar kudaden gudanar da ayyukan da aka ware a cikin kasafin.
“Idan ka duba kasafin kudin ana yinsa a rarraba masa hannu, amma kafin kudin ya fito a fara gudanar da ayyuka sai ka ga ya kai wajen wata uku ko ma fiye, ka ga sauran wata tara kenan, a cikin wata taran ma ana samun tsaikon isar kudade daga hannun gwamnati zuwa wurin da za a yi aikin, tsaikon kai kudin da aka ware zuwa bangarensa na iya kawo nakasu kusan kowani bangare na kasafi kamar su bangaren ilimi, gyare-gyaren hanyoyi da sauran bukatu ciki har da na lafiya sun dogara ne daga sako kudaden da ke cikin kasafin a kan lokaci.
“Idan ana samun tsaiko za ka ga har shekara ta kare abun da aka shirya za a kashe ma wani bangare sai ka ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
“Kowani bangare na iya samun nasara idan aka samu nasarar shawo kan matsalar jinkirin kai kudade wuraren da za a aiwatar da ayyukan da aka tsara a cikin kasafin.”
Don haka ne, ya shawarci gwamnati da cewa, muddin tana son taimaka wa tattalin arzikinta da ci gaban kasar nan, a tabbatar an aiwatar da abubuwan da aka tsara cikin kasafin kudin da magance matsalar rashin bayar da kudade a kan lokaci domin gudanar da ayyuka a kan lokaci.
“Sau da yawa sai ka ga an fara aiki amma har shekarar ta kare ko kusan rabi ba a yi ba kuma a sake yin wani kasafin na wata shekara haka abun zai ci gaba da tafiya. Fatanmu dai shi ne wannan gwamnatin ganin irin yadda al’umma suka shiga irin wannan halin lallai gwamnati ya kamata ta taka rawa sosai ta tabbatar da cewa wannan kasafin an yi aiki da shi cikin wannan shekarar kuma yadda ya kamata,” ya karkare.