Shugaban kasa, Bola Tinubu ya umurci dukkan ma’aikatu da rassan gwamnati da su bayar da rahoton aikin kasafin kudi na wata-wata ga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, wanda hakan zai tabbatar da sahihancin kwazonsu.
Umarnin ya zo ne bayan da Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudi na 2024 a ranar Litinin da ta gabata a gidan gwamnatin jim kadan bayan ya dawo Abuja daga Legas.
Da yake jawabi a wajen rattaba hannu kan kasafin kudin, shugaban kasa ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a bi diddigin aiwatar da kasafin kudin yadda ya kamata tare da sanya ido sosai a kai.
- Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5
- Xi Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Iran Bisa Munanan Hare-haren Ta’addanci Da Aka Kai A Kasar
“Dukkan hanyoyin da hukumomi za su bi domin tabbatar da aiwatar da aiki tukuru kamar yadda yake a cikin kasafin kudi.
“Mun umurci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su dunga bayar da rahoton ayyukan kasafin kudi na wata-wata ga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, wanda hakan zai tabbatar da sahihancin gwazonsu.
“Ministan kudi zai gudanar da bita akai-akai tare da tawagar masu kula da sha’anin tattalin arziki, sannan zan jagoranci taron majalisar gudanar da tattalin arziki na lokaci-lokaci,” in ji shi.
Manyan abubuwan da aka fi bai wa kaso mai yawa a cikin kasafin kudin 2024 na naira tiriliyan 28.7 sun hada da tsaro, samar da ayyukan yi, inganta tattalin arzikin kasa, inganta yanayin zuba jari, bunkasa rayuwar mutane, rage talauci da kuma samar da tsaron kasa.
Shugaban kasa ya jaddada kudurinsa na inganta harkokin zuba jari da samar da al’umma mai bin doka da oda ba tare da fifita wani mutum kan doka ba, inda ya fara da wasu muhimman gyare-gyare a bangaren shari’a, wanda aka zuba wa kudaden a cikin kasafin 2024.
“Bayar da kudade ga bangaren shari’a babban kuduri ne a kokarinmu na tallafa wa al’umma wajen gudanar da adalci da bin ka’idoji. An kara kudade ga bangaren shari’a daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342,” in ji shugaban kasa.