Ministan Yada Labarai da Al’adu na Kasa, Lai Mohammed, ya ce jam’iyyar PPD ta gaza kawo karshen Boko Haram a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbu mulki a shekarar 2015.
Mohammed ya bayyana haka ne a matsayin martani ga wani tsokaci da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi game da Boko Haram.
- Sin: Afrika Ba Fagen Dagar Takarar Kasashen Yamma Ba Ce
- Majalisar Dokoki Ta Bai Wa NNPC Mako Daya Ya Kawo Karshen Karancin Mai
Atiku, ya ce gazawar gwamnatin tarayya na kawo karshen ‘yan tayar da kayar baya ya daure masa kai.
Da yake mayar da martani a ranar Talata, Mohammed ya ce ya kamata Atiku ya tambayi PDP dalilin da ya sa ta kasa yakar Boko Haram har suka tada bam a harabar Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja.
“Shekaru shida har zuwa 2015, lokacin da gwamnatinmu ta karbi mulki kuma ta gaji ‘yan Boko Haram, PDP ko kadan ta gaza yunkurin ganin bayansu.
“Alhaji Atiku, wanda a lokacin yana zaune a Abuja kafin ya wuce zuwa sabon gidansa a Dubai, ya kamata ya tambayi jam’iyyarsa ta PDP, yayin da ta bai wa ‘yan Boko Haram damar kai hare-hare a hedikwatar ‘yansanda, harabar Majalisar Dinkin Duniya, cibiyoyin kasuwanci da tashoshin motoci a Abuja,” in ji Mohammed.