Tsohon dan wasan tawagar Kasar Kamaru, Samuel Eto’o, ya ce daya daga cikin kasashen Afirka za ta iya lashe gasar cin kofin duniya da za a fafata a Kasar Qatar wanda za a fara daga ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disamba, 2022.
A tarihi dai babu wata kasa daga Afirka da ta taba wuce zagayen kusa dana kusa dana karshe (quarter-finals) a gasar ta kofin duniya kuma kasashe uku ne kawai suka taba zuwa wannan matakin.
A gasar da aka buga a shekarar 1990, kasar Kamaru ta je matakin kusa dana kusa dana karshe, sannan kasar Senegal ta je a shekarar 2002, sai Ghana a shekarar 2010 da aka buga a Afirka ta Kudu.
Sai dai Eto’o, wanda wakilin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ne yanzu haka a Kasar Ghana, inda yake ran gadin wayar da kan kasashen Afirka a kan tsare-tsaren gasar ta bana ya ce, wannan lokacin na kasashen Afirka ne ba kawai su je wasan kusa dana kusa dana karshe ba, har ma suje su lashe gasar.
Eto’o dai ya wakilci kasar Kamaru a gasar cin kofin duniya har sau hudu, a shekarar 1998, da 2002 da 2010 da kuma 2014.
A wannan lokacin, kasashe biyar da suka hada da Kamaru da Ghana da Morocco da Senegal da kuma Tunisia ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar.