Yayin da aka cika shekara 1 da barkewar sabon zagaye na rikicin Isra’ila da Palasdinu a ranar 7 ga wata, Baitul malin Amurka ta kakabawa wasu daidaikun mutane da kamfanoni a wasu kasashe takunkumai, bisa hujjar suna samar da kudi ga kungiyar Hamas. Baya ga haka, a karshen watan Satumba, Amurka ta sake samar da tallafin soji na dala biliyan 8.7 ga Isra’ila.
Don gane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau Laraba cewa, ba makamai da takunkumai ake bukata wajen warware rikicin Isra’ila da Palasdinu ba, sai dai kyakkyawan kudurin siyasa da matakai na diplomasiyya.
Har ila yau, a martaninta don gane da shirin Isra’ila na kaddamar da harin ramuwar gayya kan Iran, Mao Ning ta yi kira ga kasashen duniya, musamman masu fada a ji, su taka muhimmyar rawa wajen kare rikicin daga ta’azzara. (Fa’iza Mustapha)