Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce alkaluma sun nuna cewa, har yanzu kasar Sin ce ke kan gaba a duniya a matsayin wacce ta fi samun jari daga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen wajen su zo su kara zuba jari.
Mao Ning ta kara da cewa, ba tare da la’akari da sauyin da za a gani a duniya ba, kasar Sin za ta cika alkawarinta na fadada bude kofarta. Kuma tana maraba da kamfanoni su zo su zuba jari tare da kara zurfafa zamansu a kasar, domin cin moriyarta da samun ci gaba na bai daya.
Da take amsa tambaya game da manufar kasar ta daukewa wasu kasashe neman visa, Mao Ning ta ce kasar ta soke neman visa ga kasashe 38 da kuma tsawaita lokacin yada zango a kasar ba tare da visa ba zuwa sa’o’i 240 ga kasashe 54. Ta ce a bara, sama da baki miliyan 20 ne suka shigo kasar ba tare da visa ba, adadin da ya karu da kaso 112 kan na shekarar da ta gabace ta. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta kaddamar da karin matakai domin saukaka shigowa kasar. Haka kuma, tana maraba da baki abokai daga fadin duniya, domin su zo su ganewa idanunsu kasar Sin ta ainihi mai kyau da bude kofa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp