A jiya Litinin ne zababbiyar shugabar kasar Namibia, Netumba Nandi-Ndaitwah ta gana da ministan harkokin wajen kasar Sin, kuma har ila yau mamba a kwamitin koli kan harkokin siyasa na jam’iyyar JKS, Wang Yi, a babban birnin Namibia Windhoek.
A ganawar tasu, Wang ya isar da sakon gaisuwar Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ga Shugaba Ndaitwah tare da taya ta murnar zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasar Namibia, kana ya yi mata fatan alheri da samun gagarumar nasara wajen gina ci gaban kasar ta Namibia.
- Xi Da Shugaban Botswana Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alaka
- Gwamnan Kano Ya Nemi A Rage Kuɗin Hajjin 2025
Wanga ya yi nuni da cewa, a bana an cika shekaru 35 da fara huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da Namibia, sai ya jaddada cewa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu na da matukar alfanu musamman ma a gaba.
Ya yi waiwaye adon tafiya a kan nasarar da aka samu a taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, watau FOCAC da ya gudana a birnin Beijing a bara, lokacin da shugaban kasar Sin ya sanar da wasu tsare-tsare guda 10 na hadin gwiwa a fannin zurfafa zamanantarwa. Wang ya bayyana kudurin kasar Sin na tafiya kafada-da-kafada da Namibia domin gaggauta aiwatar da abubuwan da aka cimma a taron, don tabbatar da dorewar ci gaban da ake samu a cikakken tsararren hadin gwiwarsu.
A nata bangaren, Shugaba Ndaitwah ta bukaci Wang ya mika sakon gaisuwarta da kuma godiya ga Shugaba Xi Jinping bisa taya ta murnar lashe zaben shugaban kasar Namibia, tana mai bayyana cewa, a shekarar 2018, kasar Sin da Namibia sun daga darajar huldodinsu na diflomasiyya zuwa cikakken tsararren hadin gwiwa wanda tabbas yana da matukar alfanun gaske.
Shugaba Ndaitwah ta kara da cewa, al’ummomin kasashen biyu sun ci gaba da sada dadadden zumuncin dake tsakaninsu kuma Namibia za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu har ma da kara daukaka shi, tare da jaddada kudurin kasar na tsayawa a kan akidar kasar Sin daya dunkulalliya.
Hakazalika, shugabar ta bayyana shirin kasar na aiwatar da sakamakon taron kolin FOCAC na Beijing da kara habaka hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, da ilimi, da aikin gona, da ababen more rayuwa da kuma albarkatun makamashi domin samar wa tattalin arzikin Namibia da walwalar jama’arta sabbin damammaki da za su amfanar da al’ummomin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)