ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Karfi Ce Ta Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

A duniyarmu ta yau, kasar Sin ta kasance amintacciyar kasa, mai daukar nauyi da dawainiyar tsarin harkokin duniya dake cike da rashin kwanciyar hankali da daidaito, da bude kofa ga dukkan nau’o’in hadin gwiwar bangarori daban-daban. Yayin da kasashen yammacin duniya ke kokarin raba gari da kasar Sin, da ma kokarin kawo tsaiko ga ci gabanta da dunkulewar duniya baki daya, yanzu kasar Sin ce ke kokarin kira da tabbatar da daidaito tsakanin bangarori daban-daban da inganta tsarin duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken “Taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya mai cike da tashin hankali” a taron tsaro na Munich da aka gudanar a ranar 17 ga watan Fabrairu.

  • Wang Yi Ya Yi Tir Da Karairayin Da Ake Yi Game Da Xinjiang A Munich
  • Al’ummar Afirka Ta Yi Maraba Da Sakon Xi Jinping Ga Taron AU Karo Na 37

Taron Tsaro na Munich (MSC) taro ne na shekara-shekara kan manufofin tsaro na kasa da kasa a birnin Munich na Jamus. Asalin taken ita ce: “Zaman lafiya ta hanyar tattaunawa”, kuma taron na wannan shekara ya maida hankali kan ko kasashen duniya sun shirya samar da zaman lafiya a aikace ko za su ci gaba da maganar baka ne kawai?

ADVERTISEMENT

Kasar Sin mai fada da cikawa, ta ba da gudummawar rundunar wanzar da zaman lafiya mafi girma duniya kuma kasa ta biyu da ta fi ba da gudummawar kasafin kudin Majalisar Dinkin Duniya. Ta yi alkawarin cika alkawuran COP28, da tafiyar da harkokin kirkirarriyar basira wato AI na duniya, da kuma zama jigon habaka harkokin duniya. Kasar Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta a Ukraine da Falasdinu. Wannan karin sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya da ya rataya a wuyan kasashen duniya yana tafiya kafada da kafada da karfin kasar Sin da tasirinta a cikin al’ummar duniya, bisa ci gaban tattalin arzikinta.

Tabbatar da tsaro a duniya ga kowa da kowa yana nufin kwarewa wajen “aiki da cikawa”. Hakan zai faru ne a lokacin da kasashen duniya suka hade waje guda domin tabbatar da tsaro na gama gari, ba wai a bar wata kasa da aikin tabbatar da tsaron duniya yayin da wasu kasashen ke mata zagon kasa ba. Kudaden da aka kashe kan aikin soji a duniya ya karu zuwa dala biliyan 2240 a shekarar 2022 kuma yana ci gaba da haurawa kawo yanzu, kamar yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a duniya. Saboda ba a kasashe wadannan kudaden ta hanyoyin da suka dace ba, shi ya sa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. An kashe kudaden ne bisa son ran kasashen yamma cike da rashin amana game da hakikanin manufarsu da muradunsu, hakan ya sanya ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi, bai kammala jawabinsa ba sai da ya jaddada tafiyar da harkokin diflomasiya bisa amana.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Don haka, a mahangar kasar Sin, hanyar da ta dace ga amincewa da juna ita ce hanyar bayyana irin gudummawar da Sin ke bi wajen daidaita harkokin duniya, da bukatunta, da kiyaye jajayen layuka masu nasaba da tashin hankali. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Ministan Labarai

Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, inji Ministan Yaɗa Labarai 

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.