A lokacin hutun bikin Bazana na bana, al’ummun kasar Sin masu dimbin yawa sun ziyarci wurare daban daban domin gudanar da yawon shakatawa.
Bayanin da ma’aikatar harkokin raya al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi, ya nuna cewa, yawan mutanen da suka yi yawon bude ido, da adadin kudaden da suka kashe a yayin lokacin hutun murnar bikin Bazara dukkansu sun kafa tarihi.
- Za A Fara Bayar Da Shudin Kati A Kwallon Kafa
- Da Ɗumi-ɗumi: Idahosa Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Edo A Jam’iyyar APC
A duk fadin kasar Sin, an kaddamar da bukukuwan taya murnar bikin Bazara har sama da dubu 150, inda mutane kimanin miliyan 669 sun kalli bukukuwan kai tsaye ko kuma ta shafin intanet.
A yayin lokacin hutun, an yi tarukan kide-kide da raye-raye, da na wasan kwaikwayo da sauransu har dubu 16.3, adadin da ya karu da kaso 52.1, bisa na makamancin lokacin bara. An kuma samu kudin shiga sama da dallar Amurka miliyan 108 a fannin kallon fina-finai, adadin da ya karu da kaso 80.09, kuma mutane sama da miliyan 6 da dubu 576 sun kalli fina-finai, adadin da ya karu da kaso 77.71.
Al’ummar Sin sun yi alla-alla wajen yin yawon shakatawa. Kuma yawan wadanda suka yi yawon bude ido, da adadin kudaden da suka kashe a yayin lokacin hutun dukkansu sun kafa tarihi.
A lokacin hutun na kwanaki 8, gaba daya mutane miliyan 474 ne suka yi ziyara a sassan kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 34.3 bisa na makamancin lokaci na bara. Kaza lika, adadin kudin da suka kashe ya kai sama da dallar Amurka biliyan 87 da miliyan 951, adadin da ya karu da kaso 47.3.
A sa’i daya kuma, adadin mutane da suka fita da shigo kasar Sin domin yawon shakatawa ya zarce miliyan 6 da dubu 800, ciki har da mutane kimanin miliyan 3 da dubu 600 da suka tafi kasashen ketare, yayin da wasu kimanin miliyan 3 da dubu 230 suka shigo kasar Sin.
A dai wannan lokaci na hutu mai tsawo, Sinawa sun ji dadin yawon shakatawa, yayin da suka kuma nuna matukar kaunarsu ga al’adun kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)