• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Adawa Da Yin Shisshigi Cikin Harkokin Gidan Kasashe Masu Tasowa Bisa Hujjar Kare Hakkokin Dan Adam

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, kasarsa tana adawa da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasashen dake tasowa, bisa hujjar kare hakkokin bil’adama, matakin da kuma ya samu goyon-baya daga sassan kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa.

Wang ya yi wannan furucin ne, yayin da yake gabatar da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya sha’anin kare hakkokin dan Adam.

  • Hu Hailan: Masaniyar Kasar Sin Da Ta Kai Matsayin Koli A Fannin Kimiyyar Kwakwalwa Da Jijiyoyi A Duniya

Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kwamitin kolin jam’iyyar dake karkashin shugabancin Xi Jinping, yana maida aikin girmamawa, gami da kare hakkokin dan Adam a matsayin wani muhimmin aiki na mulkin kasa, don samar da ci gaba ga sha’anin kare hakkokin dan Adam na kasar Sin.

Wang ya kara da cewa, kasarsa na nuna kwazo, wajen halartar ayyukan kare hakkokin dan Adam na duk duniya, kuma har sau uku kwamitin kula da hakkokin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kudirin da kasar Sin ta gabatar, dangane da gudummawar da ci gaba ya bayar, ga more dukkanin hakkokin dan Adam, gami da fadada hadin-gwiwa a fannin hakkokin dan Adam.

Hakan na nufin ra’ayoyin kare hakkokin dan Adam ta hanyar samar da ci gaba, da fadada hadin-gwiwa ya shiga zukatan al’ummomin kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Wang ya ce, kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarorin kasa da kasa, domin samar da ci gaba ga hakkokin dan Adam na duniya, da kara kirkiro makoma mai haske. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar
Daga Birnin Sin

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Next Post
‘Yan Wasan Real Madri 10 Ne Suka Taba Lashe Ballon d’Or

‘Yan Wasan Real Madri 10 Ne Suka Taba Lashe Ballon d’Or

LABARAI MASU NASABA

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

October 15, 2025
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.