Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana cewa, kasar Sin tana da muradin karfafa hadin gwiwa na shirin Ziri Daya da Hanya Daya, watau BRI a tsakaninta da Masar a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kudi, da masana’antu, da sabbin makamashi, da kimiyya da fasaha, da kuma mu’amalar al’adu da cudanyar jama’a.
Li wanda ya bayyana haka jiya Alhamis, yayin ganawarsa da shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi, ya kuma ce, kasar Sin tana son ci gaba da kara azamar cimma burin gina al’ummar Sin da Masar mai makoma ta bai-daya a sabon zamani.
- FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
- Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba
Har ila yau, firaministan na kasar Sin ya ce, a shirye kasar take ta bi sahun Masar wajen saukaka kuncin da jama’a ke ciki, da hana barkewar rikici, da rura wutar rikici, da kara zage damtse ba tare da kakkautawa ba wajen lalubo bakin zaren warware matsalar Falasdinu.
A nasa bangaren, El-Sisi ya ce, kasar Masar ta tsaya tsayin daka wajen bin ka’idar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, kuma tana son ci gaba da mu’amala mai kyau ta kut da kut a matakin koli da kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwar BRI a tsakaninsu.
Kazalika, El-Sisi ya ce, Masar tana goyon bayan jerin shirye-shirye na duniya da shugaba Xi ya gabatar, kuma ta kuduri aniyar karfafa damawa da bangarori daban daban tare da kasar Sin domin kara matse kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp