Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum da ya gudana a yau 26 ga wata, lokacin da yake amsa tambayoyi game da TikTok cewa, matsayin kasar Sin kan batun TikTok a bayyane yake.
Gwamnatin kasar Sin tana mutunta ra’ayoyin kamfanoni, kuma tana farin cikin ganin suna gudanar da shawarwarin kasuwanci bisa ka’idojin kasuwa da cimma matsaya da suka dace da dokokin kasar Sin da kuma daidaita moriyarsu.
Ana fatan bangaren Amurka zai samar da yanayin kasuwanci mai bude kofa, cikin gaskiya da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin domin su zuba jari a Amurka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp