Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, nan ba da jimawa ba, za ta yi karin haske game da ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka a kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ne ya bayyana haka a yau, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, bayan an nemi jin ta bakinsa game da tsokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi yayin ziyararsa a Shanghai. Wang Wenbin ya bayyana cewa, sun riga sun gabatar da makasudin ziyarar jami’in na Amurka, kwanaki biyun da suka gabata, tare kuma da bayyana matsayin kasar Sin kan batun.
- Xi Ya Yi Kira Ga Chongqing Da Ya Rubuta Nasa Tarihi Cikin Aikin Zamanantar Da Kasar Sin
- Kasar Sin Ta Bayyana Tarin Rarar Da Take Da Shi Ta Albarkartun Mai Da Iskar Gas
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai aiwatar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya bisa ka’idojin kasuwa, haka kuma ta kasance mai nacewa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori da dama da kuma aiwatar da ka’idojin hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) yadda ya kamata. A cewarsa, ana fata bangaren Amurka zai martaba ka’idojin takara bisa adalci da biyayya ga ka’idojin WTO da hada hannu da kasar Sin wajen samar da kyakkyawan yanayin raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu cikin aminci.
Har ila yau, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da tallafi mai yawa na yaki da cutar cizon sauro ta Malaria ga kasa da kasa, ta hanyar amfani da maganin Artemisinin wajen samar da magunguna da tallafin kwararru da ginin cibiyoyin yaki da cutar da horar da jami’ai. Ya ce, a nahiyar Afrika, shirye-shiryen yaki da cutar da magunguna da dabarun kasar Sin, sun samar da fatan rayuwa ga mutanen nahiyar da dake fama da cutar. Ya kara da cewa, kasar Sin na dogaro da cibiyar bincike da horo kan kawar da cutar Malaria ta MDD, wajen horar da sama da jami’an lafiya da masana 2,000 daga kasashe da yankuna 85, game da kandagarki da takaita cutar Malaria da sauran cututtuka masu yaduwa. A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), kimanin mutane miliyan 240 a yankin kudu da hamadar Sahara kadai, sun amfana da hadin maganin Artemisinin.
Haka zalika, Wang Wenbin, ya ce ci gaba da yaki a Gaza, abu ne da ba za a lamunta ba, kuma kisan gillar da ake wa yara da mata, abu ne da ba za a yi hakuri da shi ba, haka kuma ba za a taba amincewa da kawo tsaiko ga yunkurin Kwamitin Sulhu na MDD na ingiza tsagaita bude wuta ba. Kasar Sin na bukatar kasashe masu ruwa da tsaki, su daina kawo tsaiko kan matakan Kwamitin Sulhun, tare da kira ga bangarorin da batun ya shafa su aiwatar da kudurin Kwamitin Sulhun mai lamba 2728, da cimma tsagaita bude wuta mai dorewa nan take kuma ba tare da gindaya sharadi ba. Bugu da kari a tabbatar da samar da agajin jin kai mai dorewa ba tare da katsewa ba, domin kawo karshen wahalhalun da al’ummar Palasdinu ke fuskanta da daina kunyata wayewar kan bil Adama. (Fa’iza Mustapha)