Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mr. Dai Bing ya bayyana a jiya Talata cewa, kasar Sin na maraba da MDD ta kara kyautata hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka (AU), a wani kokari na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.
A gun taron kwamitin sulhu game da “hadin gwiwar MDD da tarayyar Afirka”, Mr. Dai Bing ya gabatar da jawabin cewa, kasar Sin na goyon bayan MDD da AU, da su inganta hadin gwiwarsu ta fannonin kiyaye zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka, da sa kaimin dorewar bunkasuwar nahiyar, da kuma gyaran tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa.
Dai Bing ya ce, ya kamata MDD da tarayyar Afirka, su ci gaba da mai da ingancin kwarewar Afirka a matsayin ginshikin hadin gwiwarsu, don kyautata kwarewar tarayyar Afirka ta fannonin yin gargadin aukuwar rikici, da magance shi da daidaita shi da sauransu.
Dai Bing ya kara da cewa, a yayin babban taron MDD na wannan karo, kasar Sin da ma kasashen Afirka sun gudanar da taron ministoci na “rukunin kasashe masu rungumar shawarar raya duniya”, inda kasar Sin ta sanar da wasu hakikanan matakai bakwai.
Kasar Sin na son hada gwiwa da kasashen Afirka wajen tabbatar da ganin matakan sun samar da albarkatu, da ma sharuda ga samun dauwamammen ci gaban kasashen Afirka. (Lubabatu)