Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin ka’idojin rarraba aiki da hadin gwiwa, da bude kofa da hada kai, yayin da take ci gaba da aiki a matsayin mai sa kaimi ga samun moriyar juna da samun nasara ga kowane bangare a fannin masana’antu da samar da kayayyaki a duniya.
He, wanda yake mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a wajen bikin bude baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing.
Mataimakin firaministan ya kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar mahada ce a bangaren masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kuma tana ci gaba da daukar matakai masu inganci don tabbatar da daidaiton ayyukan masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, tare da ba da gudummawa wajen zurfafa hadin gwiwar masana’antu da samar da kayayyaki, da kuma kara matse kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp