A matsayin ta na kasa mai dogon tarihi, da wayewar kai na tsawon shekaru fiye da 5000, kasar Sin ta fahimci darajar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Saboda haka, tun kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin shekaru 75 da suka wuce, kasar ta ci gaba da kokarin zamanantar da kanta ta hanyar lumana, tare da samar da dimbin gudunmawa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki a duniya, da kare tsare-tsaren kasa da kasa.
A shekarar 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar tabbatar da tsaron duniya, don samar da tunani mai amfani ga aikin neman samun tsaro da zaman lafiya masu dorewa a duniya.
- Wakilin Sin Ya Bukaci Sassan Somaliya Da Su Kara Azamar Warware Sabani Ta Hanyar Tattaunawa
- Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Za Ta Kawo Sabbin Damammaki Ga Duniya
Sai dai tushen zaman lafiya shi ne ci gaban tattalin arziki. Don neman cimma muradin raya tattalin arzikin kasashe daban daban, kasar Sin ta gabatar da shawarar gina “Ziri Daya da Hanya Daya” (BRI) tare. Sa’an nan cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, kasar ta kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa tare da kasashe fiye da 150, da kungiyoyin kasa da kasa 32, duk a karkashin inuwar tsarin shawarar BRI.
Ban da haka, a shekarar 2021, kasar Sin ta gabatar da shawarar neman tabbatar da ci gaban tattalin arziki a duniya. Zuwa yanzu, kasashe fiye da 100, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 20, sun nuna goyon baya ga shawarar, inda wasu kasashe 82 suka shiga kungiyar “abokan shawarar raya tattalin arzikin duniya”.
Tabbas kasar Sin ba za ta taba sauya matsayinta ba, na neman samun ci gaban kasa cikin lumana, da hadin gwiwa, da kulla zumunta tare da sauran kasashe, da neman samun ci gaban kasashen duniya na bai daya. (Bello Wang)