A jiya Talata, Mataimakin firaminitan kasar Sin He Lifeng ya bayyana cewa, kasar Sin tana kara inganta kudurinta na bude kofa a sashen hada-hadar kudi tare da yin maraba da kamfanonin zuba jari na kasashen waje domin zurfafa hadin gwiwar cin moriyar juna.
Ya bayyana haka ne a birnin Beijing a yayin da yake ganawa da shugaban kamfanin Invesco na kasar Amurka Andrew Schlossberg.
A tsokacinsa, Schlossberg ya ce yana da yakini a game da habakar kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin, yana mai bayyana cewa kamfaninsa na da muradin shiga a dama da shi a bangaren zurfafa gyare-gyaren da kasar Sin ke yi domin fadada hadin gwiwa da kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)