Rahotannin da aka ruwaito na cewa, taron kolin G20 da zai gudana a birnin New Delhi na kasar Indiya nan bada jimawa ba, zai amince kungiyar tarayyar Afirka wato AU ta zama membar kungiyar ta G20.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana a yau Alhamis cewa, Sin kasa ce ta farko da ta bayyana goyon-bayanta a fili ga AU don ta shiga cikin G20, kuma a wajen shawarwarin shugabannin Sin da Afirka da aka yi kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake nanata cewa, kasarsa za ta goyi bayan AU don ta zama memba a kungiyar G20.
Sin da AU muhimman aminan juna ne dake himmatuwa wajen raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da tabbatar da adalci da gaskiya a duniya. Har kullum kasar Sin na marawa AU baya, don ta kara taka muhimmiyar rawa a fannin daidaita harkokin kasa da kasa. (Murtala Zhang)