Kasar Sin ta gabatar da wani shirin gaggauta kara gina karfinta a bangaren aikin gona tsakanin shekarar 2024 zuwa ta 2035.
Shirin, wanda kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwa ta kasar suka fitar, ta sanya burin cimma nasara ta a-zo-a-gani, wajen gina karfin kasar a aikin gona zuwa shekarar 2027.
Haka kuma, zuwa shekarar 2027, shirin na da burin ganin an samu muhimmin ci gaba ta kowacce fuska a bangaren raya yankunan karkara da shiga wani sabon mataki na zamanantar da aikin gona da yankunan karkara.
Zuwa shekarar 2035 kuma, shirin na burin samun ci gaba mai inganci a wadannan bangarori, tare da kafuwar tsarin rayuwa na zamani a yankunan karkara. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp