Kasar Sin ta ba da gudummawar kayayyakin more rayuwa masu amfani da mafi karancin makamashi ga kasar Masar, domin taimakawa wajen inganta sauye-sauyen kare muhalli, da daidaita yanayin kasar ta arewacin Afirka.
Ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin ce ta bayar da wannan gudummawar da ta hada da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana, da kwan fitilu na LED, da na’urorin gida masu amfani da hasken rana, da na’urorin sanyaya daki masu amfani da karancin makamashi, domin inganta muhallin kasar Masar yayin da suke amfani da wadannan kayayyaki.
A yayin bikin mika kayayyakin da aka yi a birnin Alkahira na kasar Masar, jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Masar wajen tinkarar sauyin yanayi ya nuna zurfin zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.
Ali Abo Sena, babban jami’in hukumar kula da muhalli na ma’aikatar muhalli ta Masar, ya shaidawa ’yan jaridun kasar Sin cewa, wannan gudummawar za ta iya taimakawa Masar ta cika alkawuran da ta dauka ta hanyar rage fitar da iskar gas mai gurbata muhalli. (Mai Fassarawa: Yahaya Babs)