Jami’in hukumar kula da harkokin kasuwanni ta kasar Sin ya bayyana a yau Juma’a cewa, ya zuwa karshen shekarar 2024, yawan kamfanoni masu gudanar da kasuwanci da suka yi rajista a kasar Sin ya karu da kashi 3.1 cikin dari idan kwatanta da na shekarar 2023, yawansu ya kai miliyan 189.
A cikin rubu’i uku na farkon shekarar 2024, kasar ta yi rajistar sabbin kamfanoni masu gudanar da kasuwanci da suka shafi haraji kimanin miliyan 7.22. Mataimakin shugaban hukumar Shu Wei ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya ce, adadin ya karu da kashi 17.4 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2023.
Ya kara da cewa, an karfafa kokarin inganta takara a fannin hada-hadar kasuwanci, tare da yin gyare-gyare kan masana’antu na gargajiya, da raya masana’antu masu tasowa, da tsara shiri kan masana’antu na nan gaba, tare da mai da hankali kan inganta juriyar tsarin masana’antu. (Mohammed Yahaya)