Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga kasashen duniya, da su gina daidaitaccen tsarin tsaro na duniya da na shiyya-shiyya. Yana mai cewa, kasarsa za ta kare ikonta ta kowa hali.
Jakadan ya shaidawa taron kwamitin sulhun MDD kan batun kasar Ukraine cewa, ya kamata dukkan kasashe, su martaba tsarin tsaro na bai daya, cikakke, da hadin kai, da kuma dorewar tsaro, tare da dora muhimmanci kan sha’anin tsaro na juna, gina daidaitaccen tsarin tsaro, mai inganci, da dorewa a duniya da shiyya-shiyya, tare da kiyaye zaman lafiya a duniya baki daya.”
Geng Shuang ya jaddada cewa, “sai fa kawai an dora muhimmanci ga tsaron wasu da kuma kare lafiyar kowa ne, tsaron kanmu zai iya tabbata a zahiri. ”
A game da matsayin kasar Sin da kuma yadda take fatan kare cikakkun yankunanta kuwa, wakilin na kasar Sin, ya bayyana cewa, wasu kasashe sun sha nanata ka’idar ‘yancin game da batun kasar Ukraine, hakan yana kara kalubalantar ikon kasar Sin kan yankin Taiwan, har ma da gangan an haifar da tashin hankali a zirin Taiwan.
Ya kuma jaddada cewa, babu wanda ya isa ya raina kudiri da karfin da Sinawa sama da biliyan 1.4 suke da shi na kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankunanta. Don haka, yana fatan kasar da abin ya shafa, za ta fahimci wannan karara, kuma ta daina wasa da wuta.(Ibrahim)