Kasar Sin ta yi kira ga dukkan bangarori su samar da kafa ta tattaunawar diflomasiyya domin warware rikicin Ukraine.
Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun ne ya furta hakan a jiya, yayin da yake bayani game da kuri’ar Sin kan daftarin kudurin kwamitin sulhu na MDD dangane da batun Ukraine, inda ya ce kasar Sin tana kira ga dukkan bangarori su kai zuciya nesa, su kuma kaucewa duk wani abu da ka iya kara zaman dar dar, tare da barin kafar warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.
An gaza zartar da wani daftarin kuduri da kasashen Albania da Amurka suka gabatar ga kwamitin, saboda kasar Rasha ta hau kujerar naki, yayin da kasashen Sin da India da Gabon da Brazil kuma, suka kauracewa kada kuri’a.
A cewar Zhang Jun, har yanzu kasar Sin tana kan bakanta na cewa, ya kamata a girmama tare da kare cikakken ‘yancin kan kasa da yankunanta, haka kuma a kiyaye ka’idojin MDD, kana a dauki halaltattun korafin dukkan bangarori da muhimmanci, kuma a goyi bayan duk wani mataki da zai kai ga warware batun cikin lumana.
Ya ce a matsayinta na kasar da ta san ya kamata, har kullum, Sin na tsayawa ne a bangaren zaman lafiya. Kuma za ta ci gaba da taka rawa mai muhimmanci wajen saukaka yanayin da warware rikicin. (Fa’iza Mustapha)