Ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta ce kasar na bayar da muhimmanci ga raya dangantakar soji tsakaninta da kasar Amurka da tuntubar juna a dukkan matakai, kuma ba a samu katsewar tuntuba ko musaya tsakanin rundunonin sojin kasashen biyu ba.
Kakakin ma’aikatar Tan Kefei ne ya bayyana hakan a yau Laraba, inda ya ce duk da haka, akwai bukatar Amurka ta samar da yanayin da ya dace na tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Da aka yi masa tambaya game da rahotannin dake cewa Sin ta ki amincewa da bukatar ganawa tsakanin shugabannin rundunonin sojin kasashen biyu a Singapore, Tan Kefei ya ce ba zai yiwu a tattauna ba tare da ka’idoji ba, kuma ba zai yiwu a yi tuntubar juna ba tare da sharadi ba.
Ya kuma nanata cewa, alhakin wahalar da ake fuskanta na tuntubar juna tsakanin kasashen biyu na wuyan bangaren Amurka.
Bugu da kari, ya ce a bangare guda, Amurka na ikirarin son karfafa tuntubar juna tsakaninsu, amma a daya bangaren, ta na watsi da bukatun kasar Sin, kana tana kirkiro tsaiko, wanda ke nuna cewa babu tsari mai dacewa ko kadan. (Fa’iza)