Kasar Sin ta gabatar da ka’idojin dake dauke da kudurinta na aiwatar da haramcin aikin kamun kifi a kogin Yangtze na tsawon shekaru 10.
A cewar daftarin ka’idojin, wanda babban ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar, haramcin kamun kifin wani muhimmin mataki ne na inganta ci gaba mai inganci a yankin zirin tattalin arziki na Yangtze da kuma farfado da kuzarin kogin da ake wa kirari da ‘uwa’ a kasar Sin.
A cewar ka’idojin, ya kamata sassan gwamnati masu ruwa da tsaki su dauki batun aiwatar da haramcin a matsayin aiki mafi muhimmanci. Haka kuma, su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu da sa ido da daukaka hanyoyin aiwatar da doka da inganta hadin gwiwa tsakanin sassa da yankuna daban-daban wajen aiwatar da dokoki.
Bugu da kari, ka’idojin sun kuma bukaci a yi kokarin matse kaimi wajen kare halittun dake fuskantar bacewa da wadanda ba kasafai a kan same su ba, a fadin kogin. Haka zalika, sun bukaci a dauki matakan farfado da muhallan halittu da karfafa karewa da kula da halittun dake bakin wurare, da gaggauta farfado da muhallin halittu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp