A yau Laraba ne ofishin yada labarai na majalisar gudanawar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai taken Hanyoyin karkara na kasar Sin a sabon zamani, wanda ke gabatar da nasarori da hangen nesa dangane da ayyukan gina hanyoyin karkara a sabon zamani, da kuma labarin kwarewar kasar Sin.
Takardar ta ce, tsawon hanyoyin karkara na kasar Sin ya kai kilomita miliyan 4.6 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 21.7 bisa na 2013, wanda kuma ya kai zagayen yankin equator sau 115. Kana, ya zuwa yanzu, kasar ta shimfida hanyoyin sufuri a yankunan karkara, wadanda ke hada yankunan karkara da birane, da hanyoyin dake ratsa cikin garuruwa, da hanyoyin kauyuka masu saukaka zirga-zirga tsakanin gidaje da gonaki.
Hakazalika, gine-gine da inganta hanyoyin karkara na ba da cikakken goyon baya ga ci gaban tattalin arzikin yankunan karkara da al’ummar kasar Sin baki daya, a cewar takardar bayanin. (Mohammed Yahaya)