Al’ummar birnin Nanjing sun yi shiru na minti daya, an kuma karar jiniya a ko’ina cikin birnin, yayin da kasar Sin ke ci gaba da gudanar da bikin tunawa na kasa karo na 9 a yau Talata, domin nuna alhini ga mutane dubu 300 da aka kashe a kisan kiyashin Nanjing.
Kisan kiyashin na Nanjing, ya faru ne a lokacin da sojojin Japan suka kwace iko da birnin a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937.
A cikin makonni shida, maharan na Japan sun kashe Sinawa fararen hula da sojoji dubu 300, da ba sa dauke da makamai, a daya daga cikin yanayi mafi muni da aka aikata a yakin duniya na biyu.
A shekarar 2014, babbar majalisar dokokin kasar Sin, ta ayyana ranar 13 ga watan Disamba, a matsayin ranar tunawa da mutanen da aka halaka a birnin Nanjing. (Ibrahim Yaya)