Kasar Sin ta harba rokar Long March-12 daga tsibirin lardin Hainan da ke kudancin kasar, wadda ta kai wani sabon rukunin taurarin dan adam na intanet zuwa sararin samaniya.
Rokar ta tashi ne da misalin karfe 4:24 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba kumbunan kasuwanci ta Hainan. Rokar ta dauki rukuni na 29 na taurarin dan adam masu zagaye kusa da doron kasa, inda suka shiga da’irar da aka tsara. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT













